Cibiyar Gargadi ta Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya (FEW Centre) ta sake fitar da sanarwar gargadin ambaliyar ruwa ga Adamawa da wasu jihohi takwas na Arewa.
Wata takardar da ke dauke da sa hannun Darakta mai kula da zaizayar kasa da ambaliyar ruwa, Usman Abdullahi Bokani, a Abuja ranar Litinin, ta bayyana cewa akwai yiwuwar wasu kauyukan Arewa za su fuskanci ruwan sama mai karfin gaske wanda zai iya haifar da ambaliya a tsakanin ranakun 25 zuwa 29 ga watan Agustan 2025.
- Za A Watsa Shirin “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” a Manyan Kafofin Watsa Labarai Na Kasashen SCO
- Burkina Faso Da Mali Sun Yi Watsi Da Taron Sojojin Afirka A Nijeriya
Bokani, wanda ya yi kira ga ma’aikatansa da ke cibiyoyin ma’aikar a jihohin da abun ya shafa da su bayar da rahoto kan duk wani sauyin yanayi a jihohinsu, ya kuma bayyana cewa, jihohin Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano da Katsina, na gaba-gaba kan yiwuwar Afkuwar ambaliyar.
Sauran jihohin da za a iya ganin ambaliyar ruwa a cikin lokacin hasashen sun hada da Sokoto da Zamfara.
Jihohin Adamawa da Katsina ne ke da mafi yawan garuruwan da ake tsammanin ambaliyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp