Yusuf Shuaibu" />

Gwamnatin Tarayya Ta Ware Wa ’Yan Fansho Har Naira Biliyan 614.92

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ware zunzurutun kudade wanda ya kai na naira biliyan 614.92, domin biyan tsofaffin ma’aikata hakkokinsu na fansho. Hukumar fansho ta kasa (PenCom) ita ta tabbatar da hakan a ranar Litinin a safinta na tweeter. Pencom ta bayyana cewa, kudaden na wata hudu ne za a biya su. Dokar hukumr ta tanadi cewa, dole a biya duk wani tsofaffin ma’aikaci hakkinsa na fansho, saboda yadda ya sadaukar kansa wajen gina kasar nan.

PenCom ta ce, “gwamnatin tarayya ta yi kokari wajen ganin an biya tsofaffin ma’aikata wadanda su ka yi ritaya daga aiki a mabambamtan hukumomin a cikin kasar nan.”

Kafin a sake kudaden a ranar Litinin, hukumar fanshon ta kasa ta shawarci tsofaffin ‘yan sanda a kan tsaikon da aka samu wajen biya su kudaden fanshonsu sama da shekara daya.

Masu amsar fanso a karkashin kungiyar masu tsafaffin jami’an ‘yan sanda sun gudanar da zanga-zanga a shekarar da ta gabata, domin sanar wa gwamnati halin da su ke ciki.

Exit mobile version