Gwamnatin Tarayya Ta Yi Korafi A Kan Tafiyar Aikin Hanyar Jigin Kasa Na Yammacin Kasar Nan

Ministan Sufuri Musta  Rotimi Amaechi  ya bayyana takaicin sa aka yadda aikin layin dogo daga jihar Legas zuwa garin Ibadon  da aka bai wa Kamfanin Cibil Engineering Construction Corporation na kasar Chana yake yin tafiyara Hawainiya. Rotimi Amaechi ya zargi dan kwangilar saboda gazar sa wajen tura ma’aikatan sa zuwa wurin aikin, a bisa uzurin da dan kwangilar ya bayar cewar sauran yan kwangilar, baza su iya aiwatar da wasu ayyukan  na aikin na layin dogon ba da aka basu. Amaechi wanda ya sanar da ha kan a ranar Talatar data wuce lokacin da yaje duba aikin na dala biliyan 1.5 dake a yankin Ologun-Eru cikin jihar  Oyo ya ci gba da cewa, in har nace na gamsu da wannan aikin to kam nayi karya. Acewar ministan, sam-sam bamu je yankin jihar Legas ba, kuma duk mun shawo kan matsalar na jihar Legas kuma dole ne in yabawa ma’aikatan gidon ruwa na jihar Legas ganin yadda suka shawo kan matsalar bututun ruwan jihar da  suka janyo babban tirniki wajen gudonar da aiki. Ya kara da cewa, bayan an samu an shawo kan matsalar, amma kamfanin na CCECC yaki dawo kan aikin sa. Da Ministan yake yin tsokaci a kan uzurin da dsn kwangilar ya bayar na jinkirin aikin ya ce, dan kwangilar ya fake ne a kan cewar sauran yan kwanglar akwai ayyukan da baza su iya yi ba. Amaechi ya buga misali da karkatar da bututun ruwa da akayi da ake sa ran za’a kammala a ranar biyu ga watan Nuwamba, amma yanzu dan kwangilar yana buktar a kara masa wasu watanni don ya kammala aikin.

Ya kara da cewa dan kwangilar ya kuma kara bayar da uzurin cewa, akwai abubuwan da ya kamata a shawo kansu kafin a canzawa butun ruwa wuri. Acewar sa, sam ni a wuri na wannan uzurin ba abin kamawa bane domin ya zama wajibi dan kwangilar ya tashi tsaye don ya kammala aikin na Ogun da Ibadon daga yankin Apapa.zuwa Ebute-Meta da sauran sassan jihar Legas. A wa’adin watan Dismba da aka sanya na kammala aikin Ministan ya ce, kar ka manta a yau shekaru uku kenen ana son a kamma aikin. A karshe ya ce kamar yadda nake yin magana da kai a yanzu akwai sauran Gadiji uku da suka rage ba’a kammala su ba zamu kuma ci gaba da yin matsin lamba don a kammala aikin a kan lokaci.

Exit mobile version