Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare ta Kasa, Misis Zainab Ahmed, ta ce gwamnatin tarayya za ta cire tallafin man fetur da ake ta cece-kuce a kan shi kafin karshen wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Zainab ta danganta jinkirin cire tallafin kamar yadda dokar masana’antar man fetur (PIA) ta tanadar a shekarar 2021, ga babban zaben 2023 da kuma kidayar al’ummar kasa da ke tafe.
- Gwamnatin Osun Ta Ayyana Ranar Juma’a A Matsayin Hutu Saboda Zabe
- An Fitar Da Takardar Bayani Kan Inganta Dokoki A Harkokin Intanet Na Kasar Sin A Sabon Zamani
Ministar ta bayyana haka ne a yayin wata ziyarar ban girma da ta kai hedikwatar VON da ke Abuja.
Sai dai a jiya gwamnatin tarayya ta bayyana cewa har yanzu ba a cimma matsaya ba kan yadda za a dakile illar shirin cire tallafin man fetur ga ‘yan kasar nan ba.
Haka zalika, ta bayyana a jiya cewa hukumar kula da albarkatun man fetur ta Ghana NPA ta cire tallafin man fetur a kasar.
A jiya ne gwamnatin Nijeriya ta dage kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023, wadda tun farko ta shirya a karshen wannan watan zuwa watan Mayu, sannan ta amince da ajandar Nijeriya ta 2050, da ke da nufin mayar da kasar nan mai karfin tattalin arziki.
Zainab ta bukaci gwamnati mai jiran gado da ta kara kudin haraji (VAT) daga kashi 7.5 yanzu zuwa kashi 10.
Ta ce cire tallafin abu ne mai wahala a siyasance da tattalin arziki da gwamnati ta dauka.
Sai dai ministar ta ce kusan kowa a yanzu ya amince cewa tallafin ba ya yi wa mutanen da ya kamata hidima kuma tsadarsa na kara gibi a gwamnatance.
Ta kara da cewa kudin tallafin litar man fetur ya kai tsakanin N350 zuwa N400, inda Nijeriya ke kashe kusan Naira biliyan 250 a kowane wata wajen bayar da tallafin.