Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta fara hana shigowar baƙin haure cikin ƙasar daga ranar 1 ga watan Agusta, 2025.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin wata ganawa da ƙungiyar tuntuɓar ma’aikata ta Nijeriya (NECA), a Abuja.
- Rasha Da Ukraine Sun Amince Da Tsagaita Wuta A Tekun Black Sea
- Yawan Ziyarar Da ‘Yan Siyasa Da ‘Yan Kasuwar Amurka Ke Kawowa Sin Ya Zo Da Mamaki
Ya ce kafin aiwatar da wannan sabon tsari, gwamnati za ta gudanar da shirin “afuwa na shige da fice” na watanni uku daga watan Mayu zuwa Yuli, don bai wa waɗanda suka riga suka shigo Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba damar daidaita matsayinsu.
Ministan ya kuma gargaɗi kamfanonin da ke hana hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (NIS) gudanar da aikinta, yana mai cewa gwamnati ba za ta lamunta da irin wannan matsala ba.
Gwamnatin ta yi kira ga baƙin haure da ke zaune a Nijeriya da su bi dokoki kafin lokacin da matakin zai fara aiki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp