Umar A Hunkuyi" />

Gwamnatin Tarayya Za Ta Raba Wa ’Yan Nijeriya Dala Milyan 322 Da Abacha Ya Sata

Gwamnatin tarayya tana kan shirin karshe na raba wa ‘yan Nijeriya dala milyan 322 da tsohon Shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abacha ya sata, ya kuma boye su a kasar Switzerland, amma gwamnatin ta sami nasarar dawowa da su.
Mai taimaka wa Shugaban kasa na musamman kan harkokin farfado da shari’a, Juliet Ibekaku-Nwagwu, ce ta bayyana hakan kwanan nan ga manema labarai yayin wata tattaunawa da ta yi da su.
Juliet Ibekaku-Nwagwu ta ce, za a biya kudaden ne kai tsaye zuwa cikin asusun bankunan matalautan kasarnan har na tsawon shekaru biyu, za kuma a bayyana lambobin mutanan da suke cin gajiyar kudaden a yanar gizo.
Ta nemi ‘yan Nijeriya da su kara hakuri, inda ta ce hukumar da za ta yi rabon kudin za ta fitar da cikakken bayani kan hakan a ranar 28 ga watan Yuni, ta kara da cewa, babu wata rufa-rufa kan yadda za a yi rabon kudin, domin kungiyoyi da manema labarai duk za su sanya ido kan yanda za a yin.
“Za a yi rajistan matalautan ne a yanar gizo, kafin kuma a biya su sai sun nuna katin su na shaida ta yadda za a rika kula da duk wani abin da aka biya. Kwabo ba za a biya ba, sai da sa hannun gwamnati da kuma bankin duniya har ma da katin shaidan kowa,” in ji ta..

Exit mobile version