Abubakar Abba" />

Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Naira Biliyan 37 Ga Masu Samar Da Mitar Kudi

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewar, zata yi amfani da damar shirin rabar da mitar wutar lantarki da hukumar sanya ido akan yadda ake rabar da wuta ta kasa ta kirkiro ta hanyar samar da naira biliyan 37 ga masu rabar da muta masu zaman kansu.

Ta kuma umarci It kamfanonin samar da wutar dasu tuntubi hukumar kula da yanayi ta kasa (NMA) don a magance kalulen da ake fuskanta a yanzu ke shafar samar da  wuta da kuma rabar da ita a lokacin damina.

Ministan wuta da ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola ne ya sanar da hakan a taron watata karo na ashirn da takwas na masu samar da wutar.

Ya yi nuni da cewar, daga yadda ake samar da wutar akwai maganar kiyasin karancin mitocin, inda ya kara da cewar maganar ya kamata a kawo karshen ta kuma a bangaren mu na gwamnati, mun saurare su da babbar murya kuma muna fatan suma masu samar da wutar suma zasu saurare su.

A cewar sa, ganin masu samar da wutar zasu ci gaba da yin karin akan samar da wutar da kuma rabar da ita, bukatar da mitocin zata karu saboda yadda aka samar da wutar haka kuma yin amfani da ita yake karuwa har da biyan bil din na wuta.

Ministan ya kara da cewar, a bisa yadda rabar da bil in wuta zai kasance wajen sanya rashin yarda da tayar da kura a tsakanin kamfanoni  masu rabar da wuta da masu yin amfani da ita domin ta hanyar mita ne za a  iya kulla yarda.

Fashola ya bayar da shawarci kamfanonin rabar da wuta da har yanzu ba su yi amfani da damar dasu hanzar ta wajen zuba kudin su da shiga da kuma tuntbar ‘yan kwangila masu samar da mitocin don a sanya su.

A cewar sa, kamfanin rabar da wuta na Yola ya kokarin samar da mitoci 400,000 a karkashin shirin, inda kuma kamfanin na Abuja, shi ma yana kokarin samar da mitoci 250,000.

Don inganta aiki a fannin, Fashola ya sanar da mahalarta taron cewar, a yanzu mana a cikin farkon yanayi ne kuma ko wanne yanayi yana zowa ne da tashi matsalar, ba wai lallai akan kadarar wuta ba harda akan kaya.

Ya yi nuni da cewar, wannan yana zamowa masu samar da wutar kalubale, a saboda haka, yana da kyau ga masu samar da wutar su dinga tuntubar hukumar yanayi ta kasa a wannan lokacin da ake ciki yanzu.

Ya yi nuni da cewar zasu kuma iya dinga duba yanayin a kafar yanar gizo ta hukumar don samun bayanai.

Majiyar mu ta ruwaito a ranar litinin cewar, Fashola ya gargadi masu samar da wutar akan yanayin na daminar bana wajen rabar da wutar.

 

Exit mobile version