Sulaiman Ibrahim" />

Gwamnatin Tarayya Za Ta Sauya BVN Da NIN – Pantami

Gwamnatin Tarayya na shirin maye gurbin lambar Banki (BVN) da sauran cibiyoyin tattara bayanai da lambar shaidar dan kasa (NIN), Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital, Dokta Isa Ali Ibrahim Pantami ya bayyana hakan.
Pantami ya bayyana hakan ne bayan lura da tsarin rajistar NIN a ofisoshin kamfanonin sadarwa a Abuja ranar Litinin.
“Na gabatar da bayani ga Kwamitin Dorewar Tattalin Arzikin Kasa kuma na ja hankalin Gwamnan CBN cewa ya kamata mu maye gurbin BVN da NIN saboda BVN manufofin banki ne kawai yayin da NIN doka ce saboda an kafa ta da doka don haka karfin doka a duk inda ka je ba iri daya bane da manufofin wata hukuma ”, in ji Ministan.

Ya ce kundin bayanan NIMC shi ne na farko a kasar nan da ya kamata kowace hukuma ta samu bayanai akai.

Ya ce: “A kwamitin NIMC, gwamnan CBN memba ne, DG DSS memba ne, Shugaban FIRS memba ne, Shugaban INEC, Ofishin mai ba da shawara kan tsaro na kasa (NSA), Hukumar Yawan Jama’a da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya. dukkansu mambobi ne na hukumar kuma wannan ya nuna muku cewa babbar matattarar bayanai ce da duk wata hukuma a kasar nan za ta yi ishara da ita”. Inji Ministan

Exit mobile version