Daga Wakilinmu
Gwamantin tarrayya ta bayyana cewa za ta yi hadin guiwa da Kungiyar Yawon Bude Ido ta MajalisarDinkin Duniya, wato, UnitedNations World Tourism Organisation da gidan talabijin na CNN don bunkasamasana’atar harkar fasaha a kasar nan.Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana hakan aJihar Lagos yayin shiga yarjejeniyar.
Alhaji Lai ya jaddada cewa yin amfani da masana’atar fim a matsayin gwaji, zata iya zamowa wata sabuwar hanyar ta kaucewa dogaro akan Man fetur a kasar nan, musamman yadda kasashen duniya kamarBirtaniya da Amurka suka tabbatar da hakan.Ya ce, “zamu fara gudanar da shirin da fitowa kashi na sha uku, wandaya hada da zabar wurin daukar fim, wanda hakan zai bamu damar nunakyawawan al’adun Najeria a idon duniya.Yaci gaba da cewa, irin sautin da za a sanya a fim din, zai nunahazakar da mutanenmu suke da ita.
Lai ya ce, za a dinga sanya shirin a kafar talabijin ta CNN don nunawaduniya irin fasahar da Allah ya albarkanci ‘yan kasar nan da ita, kumamasu ruwa da tsaki a kan harkar fasaha ne, zasu zabo ’yan Najeriya masufasahar.”
A karkashin yarjejeniyar dai, masana’antar ta fim zata yi amfani da madubin hangen nesa da kasar nan zata yi amfani da su wajen habakaal’adu da yawon bude ido na kasar nan.