Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya tsayar da farashin takin zamani, samfurin NPK kan Naira 13,000 domin noman bana.
A jawabin da ya yi yayin kaddamar da shirin takin, Buni ya yi gargadi cewa iya manoma kawai za a sayar wa da takin.
“Ina mai gargadar ku cewa gwamnati ba za ta lamunci yin sama-da-fadi ko kuma karkatar da takin ko ma zagon-kasa ba.
“Jami’an gwamnati da a ka amince da su sayar da kayan, su tabbata sun raba shi daidai a dukkanin Kananan Hukumomi 17 na jihar,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga manoma da kada su sayar da takin saboda sun same shi a farashi mai sauki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp