Gwamnatin Zamfara Ta Bada Ayyuka Sama Da Na Biliyan Biyar Ga Hukumar ZUBEB

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin gwamna Bello Muhammad Matawale ta bada ayyukan a hukumar kula da makarantun firamare na sama da naira biliyan biyar.

Shugaban hukumar na jihar ,Alhaji Abubakar Aliyu Dan Madamin Maradun ne ya bayyana haka a lokacin ba ‘yan kwangilar takardar shedar fara aikin a fadar gidan gwamnatin da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Dan Madamin Maradun ya bayyana cewa’ ayyukan da hukumar ta bada kwangilar sun kunshi na ,sabin Aji dari shida da sha takwas sai kuma gyaran Ajujuwa dari da arbain da uku da kuma dakin bayan gida talatin da Tara.sai kuma Kujeru dubu goma sha biyu da dari takwas da goma sai kuma taibura dari tara da sitin da Kuma cibiyar kowan Na’ura mai kwakwalwa watau (ICT) goma sha biyu.da dai sauran su.

A nasa jawabin Gwamna Bello Muhammad Matawale ya bayyana cewa’ wadannan ayyukan an bada su ne ga ‘yan jihar Zamfara kuma yana daga cikin sharudan cewa’ duk ayyukan bamu yarda a gayyato wani mai aiki daga wajan jihar ba ko sawo kayan aikin daga wajan jihar ba duk abunda dan kwangila zai saya akwai shi a jihar haka kuma suma.muna da ma’aikatan an an cikin jihar dan haka ba zamu lamuncin wani ya sawo kayan aiki ko mai aiki daga wajan jihar ba, duk Wanda yayi haka zamu amshe kwangilar muba mai kinshin jihar da alummar jihar.

Anasu jawabin daya daga cikin ‘yan kwangilar ,Alhaji Bashir Bukuyum ya bayyana cewa’ zasu wannan kaidar na sayan kayan aiki a jihar Zamfara da kuma daukar ma’aikata a cikin jihar da garuruwan da mu me aiki.

Exit mobile version