Gwamnatin Jihar Zamfara ta kafa dokar hana fita a fadin jihar sakamakon rikicin da ya barke bayan sanar da sakamakon zaben gwamna.
Kwamishinan Yada Labarai na Zamfara, Ibrahim Dosara ne, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, kimanin sa’o’i 24 da bayyana sakamakon zaben gwamna.
- Lokaci Ya Yi Da Zan Zama Shugaban Majalisar Dattawa, In Ji Uzor Kalu
- APC Ta Bai Wa INEC Kwanaki 7 Don Sake Nazarin Sakamakon Zaben Gwamnan Kano
“Gwamnatin Jihar Zamfara ta lura da yadda ake barnatar da dukiyoyi da kaddarorin gwamnati da na al’umma, inda ake ci gaba da raunata wasu ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, da sunan murnar bayyana sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a jiya,” in ji Kwamishinan
“Rahotanni da gwamnati ta samu sun nuna cewa an yi asarar rayuka, an lalata gidaje da raunata mutane, an kuma yi wa shaguna fashi. Domin kiyaye wadannan ayyuka, gwamnati ta ga ya zama wajibi ta sanya dokar hana fita a fadin jihar daga karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe har sai an samu zaman lafiya.
“Saboda haka an umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da bin ka’ida,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp