Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala shirye-shiryen raba dabbobi kyauta ga mata a jihar.
Kodinetan shirin Fadama III na jihar, Ismael Abubakar Ribe ne ya bayyanawa manema labarai haka a lokacin da yake amsa tambayoyi a ofishinsa da ke Gusau.
- Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Ayyukan Gina Cibiyoyin Masan’antu Da Gina Asibitin A Kauran Namoda
- Gwamnan Ondo Ya Sauke Kwamishinonin Jihar Baki ÆŠaya
Ribe ya bayyana cewa, an zabo kungiyoyin manoma 8 ne daga kowace Karamar Hukumar amma karamar hukumar Gusau an zabo kungiyoyi 11 saboda itace hedikwatar Jihar da tafi yawan al’umma.
Ya kara da cewa, tuni Gwamnan Jihar, Dauda Lawal ya kaddamar da rabon taki da kayan Noma kyauta a kananan hukumomin da nufin habbaka aikin noma a jihar.
“Gwamnatin Zamfara ta damu matuka da halin da mazauna karkara ke ciki musamman awannan lokacin, za a ba kowane akuya 3 – Namiji da mata biyu.