Bayan da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000, wasu gwamnonin jihohin Nijeriya, sun bayyana cewa ba za su iya biyan wannan sabon albashin ba saboda matsalolin kudi.
Ga jerin gwamnonin:
- Lokuta Da Yawa Nakan Dakata In Yi Kuka Ma’ishi Kafin Na Ci Gaba Da Rubutu – Fatima Gurin
- Nazari Kan Dabarun Koyarwa Da Amfaninsu
Jihar Gombe: Gwamna Inuwa Yahaya
Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya ce gwamnatinsa ba za ta iya biyan sabon albashin Naira 70,000 ba saboda kudaden da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya ba za su isa ba.
Yahaya, wanda kuma shi ne shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, ya ce biyan tsohon mafi karancin albashi na Naira 30,000 yana yi musu wahala.
Ya bayyana cewa da yawa daga cikin jihohi ba za su iya biyan karin albashin ba, duk da karin kudaden da suka samu daga gwamnatin tarayya a kwanan nan.
Jihar Nasarawa: Gwamna Abdullahi Sule
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, ya yanke shawarar jinkirta aiwatar da sabon tsarin mafi albashi na Naira 70,000 har zuwa shekarar 2026.
A baya, ya yi alkawarin fara biyan sabon albashin a wannan watan, tare da biyan bashin watannin da suka wuce.
Duk da haka, ya bayyana cewa jihar na bukatar kimanin Naira miliyan 200 domin biyan ma’aikata, wanda ya ce hakan ba zai yiwuwa jihar ta fara biyan sabon albashin a yanzu ba
Jihar Kogi: Gwamna Ahmed Usman Ododo
Gwamna Ahmed Usman Ododo na Jihar Kogi bai yanke shawara kan ko yaushe gwamnatinsa za ta fara biyan sabon mafi karancin Naira na 70,000 ba.
Kwamishinan kudi na jihar, Ashiwaju Ashiru Idris, ya ce ba a sanya ranar fara biyan sabon albashin ba.
Damuwar Masana’antu Masu Zaman Kansu
Kungiyar Masana’antu Masu Zaman Kansu (OPS), ita ma ta bayyana damuwa kan sabon albashin na Naira 70,000.
Sun ce zai yi wahala kamfanoni su iya biyan wannan sabon albashi ba tare da samun taimako na musamman ba.
Adewale-Smatt Oyerinde, mai magana da yawun Kungiyar Masu Daukar Ma’aikata ta Nijeriya (NECA), ya nuna damuwa kan yadda sabon tsari albashin zai jefa kamfanoni cikin matsalar kudi.
Martanin Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC)
Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) a Jihar Legas, ta fayyace cewa mafi karancin albashin Naira 35,000 da ake biya a halin yanzu daban ne da sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 da mayar doka kwana nan.
Funmi Sessi, shugaban NLC na Jihar Legas, ya yi kira da a samar da tsarin albashin da ya dace da nau’ikan ayyuka da matakan albashi daban-daban.
Wannan yanayin ya bayyana matsalolin kudi da jihohi da masana’antu daban-daban ke fuskanta wajen kokarin gyara tsarin albashinsu zuwa sabon mafi karancin albashi.