Fasto Umo Bassey Eno ya samu lambar yabo ta Gwarzon Gwamnan Shekara ta 2024 ta Jaridar Leadership, saboda jagorancinsa na hangen nesa da kuma saurin aiwatar da tsare-tsaren Noma da Ci gaban Karkara da samar da Ababen More Rayuwa, Tsaro da Ƙarfafa Wa Jama’ar jiharsa (ARISE Agenda).
Wannan Shiri (ARISE Agenda) ya shafi ɓangarori masu muhimmanci kamar lafiya da ilimiilimi da tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi da sauransu, wanda ya hakan ya yi tasiri a Jihar Akwa Ibom cikin watanni 15 kacal na mulkinsa. Ta hanyar ayyana muradunsa a fili da cimma nasarori masu gamsarwa, Fasto Eno, ya tabbatar da cancantarsa na samu wannan babbar lambar yabo.
- Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati 2024: Shugaban Kwastam, Alh. Bashir Adewale Adeniyi
- Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke
Umo Eno shi ne gwamnan farar hula na huɗu a tarihin Jihar Akwa Ibom mai shekaru 37 tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999. Fasto ne a Cocin All Nations Ministry International Church, bayyanarsa a matsayin gwamna abin mamaki ne, wanda ya sa ake masa laƙani da “Golden Boy” saboda kyawun fuskarsa da kuma tafiyar siyasarsa mai cike da al’ajabi. An gano bajintarsa a siyasance ta hannun, tsohon Gwamna Udom Emmanuel, wanda Eno ya fara siyasarsa ta hanyar zama Kwamishinan filaye a jihar.
A lokacin da tsohon Gwamna Udom Emmanuel ya kusa barin mulki, ba tare da ɓata lokaci ba ya zaɓi Eno a matsayin wanda zai gaje shi duk da yawan masu neman wannan matsayi. Wannan sanarwa ta girgiza mutane da dama da suke tsammanin zaɓar wanda ya yi fice a siyasar jihar. Duk da haka, Eno ya samu karɓuwa sosai, ba kawai daga Kiristoci da abokan tsohon gwamnan ba, har ma daga jama’ar Akwa Ibom da yawansu ya kai miliyan 7.2. Duk da cewa akwai shakku a zukatan wasu saboda rashin daɗewarsa a harkar siyasa, amma ya kawar da wannan shakkun ta hanyar juriya da jagorancinsa.
Ko da yake ya fuskanci zarge-zarge a siyasa, ciki har da kiransa da “wanda bai da ilimi,” Eno ya fuskanci kalubalen, ta hanyar jajircewa da ƙwarewa a matsayinsa na shugaba. Tafiyarsa a harkar siyasa, wanda ba kasafai aka san shi da ita ba, ta zama misalin yadda mutum zai iya nasara duk da ƙalubalen da zai fuskanta.
A ranar 29 ga watan Mayu, 2023, lokacin rantsar da shi, Eno ya bayar da labarin rayuwarsa mai ban sha’awa, inda ya ruwaito yadda ya tashi cikin ƙunci a matsayin ɗan wani ɗan sanda da kuma mahaifiya mai ƙoƙarin kula da iyalanta bayan mutuwar mahaifinsa. Ya tashi a barikin ‘yansanda, ya yi karatu da sayar da lemo a Filin Jirgin Sama na Legas domin tallafa wa mahaifiyarsa da ‘yan uwansa. Ya ruwaito cewar, “Da wani ya faɗa min zan zama gwamna, da na ce masa ya je asibiti domin tabbas yana fama da ciwon maleriya mai tsanani ko kuma ya ruɗe.” Yau, mutumin da ya tashi a wannan yanayi ya zama gwamnan Jihar Akwa Ibom a zahiri.”
Mulkin Eno ya tabbatar da alƙawarin jagoransa, Udom Emmanuel, wanda ya ce, “Mutumin da zai zo bayana zai yi abubuwa masu tasiri sama da waɗanda na yi.” Ta hanyar tsarin ARISE Agenda, Gwamna Eno ya mayar da hankali kan samar da abinci da samar da ayyukan yi da kuma samar da tsaro mai inganci, wanda ya mayar da Akwa Ibom wata mafaka ga masu yawon buɗe ido da masu zuba jari da kuma baƙi.
Wannan ci gaba ya bunƙasa samun kuɗaɗen shiga na jihar, wanda ya ƙara mata matsayi a matsayin babbar jiha mai arziƙi a yankin Neja Delta.
Nasarar da Gwamna Eno ya samu ta ja hankalin mutane da dama, har ma a matakin ƙasa. Duk da cewa Akwa Ibom tana ƙarƙashin mulkin jam’iyyar adawa, ya samu haɗin kai daga manyan mutane irin su Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio. Jagorancinsa ya kawo ƙarshen rigingimun siyasa da suka daɗe suna hana Jihar Akwa Ibom samun ayyukan gwamnatin tarayya da wasu tallafi, inda ya kawo wani sabon salo na haɗin kai da ci gaba a jihar.