Yi Wa Marasa Lafiya Aiki Wani Abu Ne Yake Bashi Sha’awa
A duk faɗin asibitocin birane da ƙauyukan Nijeriya, sunan Dr Seidu Adebayo Bello ya zama daidai da waraka ga al’umma.
Ta hanyar aikinsa na gidauniyar Cleft and Facial Deformity Foundation (CFDF), ya ɗauki aikin tiyata na ƙwararru zuwa matsayi nag aba inda ya yi wa mutane fiye da 2,600 aikin da ya canza rayuwarsu, inda yanzu suna nan suna ta mjurna da yi masa fatan alhairi.
- Sheriff Oboreɓwori: Gwamnan Da Ya Ginu Kan Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Al’umma
- Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal
“Kiwon lafiya ba aikin jinƙai8 kaɗai ba ne aiki ne da dawo da mutunmcin al’umma.
Manufar mu ya taso ne daga buƙatar samar da daidaito a cikin al’umma.
Aƙidar Dr Bello abu ne mai saƙin gaske kuma akwai hikima a ciki sosai. Shi ne kuma samar da ingantacciyar kiwon lafiya wand aba wai sai kana da kuɗi mai yawa ba.
Tsarinsa shi ne haɗa yi wa mutane aiki, ilimantar da su tared fda kuma tsugunar da su. Wannan mataki ne da yake tabbatar da an samun cikin gaggawa da kuma sauƙin gaske..
Daga Legas zuwa Kano, daga Ondo zuwa Kuros Riba, kungiyar CFDF tana tafiya da kayan aiki na tafi da gidanka da kuma rundunar likitoci masu tiyata na sa kai, masu aikin jinya, da ma’aikatan jinya. Kowace manufa asibiti ce mai motsi – duba marasa lafiya, yin hadaddun tiyata, da bayar da shawarwari da tallafin abinci mai gina jiki ga iyalai waɗanda a da suna tunanin warkarwa ba ta isa ba.
A ƙarƙashin shugabancinsa, gidauniyar ta zama wani samfur na yadda za a gudanar da samar wa da al’umma kiwon lafiya mai sauƙi kuma mai inganci, musamman tiyata a fuska.
Canza Tsari Ba Canza Fuska kawai Ba
Cutar Cleft lips da palates sun daɗe suna takura wa al’umma. Yara na kunyar fita cikin mutane, ana kuma tsangwamar iyaye mata da iyalai inda ake ɗora musu lafin aukuwar cutar.
Ayyukan Dr Bello suna kula da waɗannan yanayi n acuta, ana kuma amfani da tiyatar da ake yi wajen yaƙar jahilci. Duk gangamin da aka ana amfani da shi wajen faɗakar da al’umma akan ainihin yadda cutar take tare da kuma ƙarfafa wa al’umma kawo mara lafira domin amagani a kan lokaci.
Ta hanyar ilimantar da al’umma da kuma bibiyar mara lafiya bayan an yi masa tiyata a yanzu an samu rage tsoro da jin kunya a zukatan mutane, mutane kuma na ƙara fahimtar cewa, wannna cut aba tsinuwa ba ne abu ne da za a iya warkar da shi ta hanyar kimiyya da fasaha.
Likitan Tiyata, Masani kuma bawan Allah
Cikakken masani kuma ƙwararren likitan tiyata a a babban asibitin fadar shugaban ƙasa, Dr Bello yana shugabanci cikin matsuwa da hangen nesa.
Mamba ne na ƙungiyoyi da dama da suka haɗa da ‘National Postgraduate Medical College of Nigeria (FMCDS), West African College of Surgeons (FWACS), International Congress of Oral Implantologists (FICOI) da kuma Global Congress of Implantology (FGCOI).
A mastayoinsa na malamai, Dr Bello ya karantar tare da sa ido a ayyukan matasan likitoci masu tasowa da dama, ta haka za a tabbatar da sun gaji irin ƙwarewarsa tare da samar wa al’umma fata na gari.
Ya kuma rubuta muƙaloli na kimiyya fiye da 35 ya kuma ƙirƙiro ‘International Craniofacial Academy (ICA) a Abuja, ya kuma ci gaba da yi wa mutane tiyata kyauta ba tare da ko sisi ba.
Abin Ya Fi Batun Ɗakin Tiyata
A wajen asibitin, Dr Bello yana da alaƙa da tushen sa. Yana riƙe da matsayin Aare musulmi na Ago Are, shugaban kungiyar ci gaban Oke Ogun (reshen Abuja), kuma ya shahara dawajen yi wa al’umma hidima.
Amma ga marasa lafiyarsa, “likita ne kawai mai sanya murmushi ga fuskan al’umma.”
Samar da Kiwon Lafiya Mai Dorewa
A shekarar 2010 aka kafa gidauniyar “ Cleft and Facial Deformity Foundation” an kuma gudanar da tiyata sama da 50 a duk yankuna shida na ƙasar nan.
Misalin haɗin gwiwarsa tare da gwamnatocin jihohi, asibitocin koyarwa, da al’ummomin gida ya tabbatar da cewa ingantaccen tsarin kiwon lafiya yana buƙatar ingantattun ababen more rayuwa.
Alƙalumma Basa Ƙarya
An yi tiyata 2,600 kyauta, An kammala ayyukan jinya 50 a faɗin Nijeriya
Ɗaruruwan ma’aikatan lafiya sun sami horo a yankunan karkara
Dubban iyalai ne aka faɗakar a kan rashin fahimtasu ga yadda cutar take.
Rayuwar Da Ke Taimakawa Motsi
Dr Bello ya zaburar da masu aikin sa kai a Yammacin Afirka don yin hidima ga marasa lafiyata hanyar daidaita tsakanin manufofi da aiki, ya nuna cewa ƙudurin likitan fiɗa ɗaya zai iya zama matakin samun nasara ga kiwon lafiyar al’umma.













