Bamanga Usman Jada, Shugaban Hukumar Kula da Yankin da suke da Albarkatun Iskar Gas (OGFZA), ya samu lambar yabo ta Leadership kan yadda ya jagoranci kawo sauyi a harkokin gudanarwar hukumar da ya ke jagoranta.
An naɗa Jada a hukumar OGFZA a cikin shekarar 2023, ya jagoranci sake lalubo yankunan da suke da albarkatun iskar gas guda biyu a jihohin Rivers da Akwa Ibom, wanda hakan ya kawo sa hannun jarin da yakai sama da dala biliyan 15 tare da samar da ayyukan yi kusan 22,000 a Nijeriya.
- Tinubu Zai Tafi Afirka Ta Kudu Daga Faransa
- Babu Gudu Ba Ja Da Baya Wajen Yaki Da Hauhawar Farashin Kayayyaki – CBN
A cikin ƙanƙanin lokacin da ya ke shugabantar hukumar, ya samar da kuɗaɗen shiga da yakai dala biliyan 24 a hukumar, ya kuma samar da hannun jari daga ƙasashen ƙetare, wanda ya ƙarfafa masana’antar mai da iskar gas a Nijeriya.
Usman Jada, Ya yi karatu a Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Yola, da kuma Jami’ar Lancashire. Ya samu gogewa da ƙwarewa a fannin kuɗi da ayyuka a ɓangaren makamashin. Alaƙarsa da cibiyoyi da kamfanoni da manyan masana’antu da ƙanana ya nuna irin sadaukarwarsa da irin burin da ya ke da shi na kawo dabaru da sababbin hanyoyin da za su samar da ci gaba, da inganta samar da kyakkyawan shugabanci a matsayin abin da ya sanya a gaba.
Yadda ya ke shugabancin hukumar ya nuna ƙwarewarsa wajen iya gudanar da jagoranci mai cike da hangen nesa, da sadaukar da kai wajen kawo ci gaban ƙasa, waɗannan dalilai ne ya sa shi zama gwarzon ma’aikacin gwamnati a Nijeriya da ya yi fice a shekarar 2024.