• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

by Leadership Hausa
4 hours ago
Kamfani

A harkar mai da iskar gas ta Nijeriya, Injiniya Gbenga Olu Komolafe, OFR, FNSE, ya yi tsayin daka kai ka ce shi wani ginshiƙi ne  kuma jagora mai jajircewa da ke tuƙa jirgin makamashin ƙasar ta cikin ruwan da ba a taɓa shigarsa ba, da hangen nesa, basira da ƙarfin zuciya.

Fiye da shekaru talatin, ya shimfiɗa hanyoyin sauyi kamar wani gwani a fannin sassaƙa dutse, yana da basirar ƙirƙira mai ɗorewa a cikin tsarin harkar man fetur na saman teku. Da zuciyarsa da hikimar dattaku, ya kasance mai tsara gini kuma mai kewayawa.

Yana ɗauke da ƙwarewa biyu a fannin sana’a, yana da tunani da ƙwarewa a fannin injiniya, kuma yana nazari da tunani mai zurfi kamar lauya.

  • Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya
  • Gwamna Lawal Ya Gwangwaje Kamfanin Sufurin Mota Na Zamfara Da Motoci 50 

A matsayinsa na shugaban farko a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur na Saman teku ta Nijeriya (NUPRC), ya kawo sauye-sauye cikin ƙwazo, ya daidaita tsarin makamashin Nijeriya da mizanin ƙwarewar duniya.

Dokar Masana’antar Mai, a ƙarƙashin kulawarsa mai basira, ta zama fitilar ci gaba, haske ga ci gaba mai ɗorewa da gaskiya a tsarin kula da harkokin masana’antar, tana haskaka tafiyar ƙasar zuwa sabon zamani na makamashi.

LABARAI MASU NASABA

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

A ƙarƙashin jagorancinsa mai hangen nesa, hukumar NUPRC ta zarce burinta na samun kuɗaɗen shiga har da kashi 84.2 cikin ɗari, tana motsawa da ƙarfafa tattalin arziki da sauyi mai zurfi a fannin masana’antar.

A matsayinsa na shugaban farko na CCE, Injiniya Komolafe ya haɗa da ƙwarewa ta injiniya da fahimtar doka cikin ƙwarewa don inganta aiwatar da Dokar Masana’antar Mai (PIA), inda ya kafa tsare-tsaren kula da aiki bisa gaskiya, ɗorewa, da bin ƙa’idar ƙwarewar duniya.

Jagorancinsa ya haifar da ci gaban fasahar zamani, inda aka gudanar da mafi fa’idar tsarin neman lasisi a tarihin Nijeriya, tare da aiwatar da manufar “Haƙowa ko Barin Filin” (“Drill or Drop”), wanda ya farfaɗo da filayen haƙar mai da suka daɗe a mace, ya kuma jawo hannun jarin da ya kai biliyoyin Daloli.

Muhimman nasarorin da aka cimma a lokacin jagorancinsa sun haɗa da:

Ƙarfafa jarin zuba hannun jari: Amincewa da Shirye-shiryen Ci gaban Filaye (Field Deɓelopment Plans – FDPs) guda 79, waɗanda ke da yuwuwar jarin da ya kusanci Dala biliyan 40, abin da ke nuna tsarin da ya ƙarfafa shigowar jarin cikin gida da na ƙasashen waje.

Ƙaruwa a samar da man fetur: An samu ci gaba mai ɗorewa a samar da man fetur, inda matsakaitan abin da ake fitarwa na yau da kullum yanzu ya kai ganga miliyan 1.68 a kowace rana, bayan kai kusan ganga miliyan 1.8 a watan Yuli 2025, wanda ke nuna mafi girman matakin fitarwa a kwanan nan, kuma yana nuna hanya ta zahiri zuwa ganga miliyan 2.5 a kowace rana nan da 2027 ta hanyar shirye-shiryen dabarun.

Daƙile satar man fetur: A shekarar 2021, matsakaitan asarar man fetur a kowace rana sun kai ganga 102,900 a rana, ko ganga miliyan 37.6 a shekara. Sai dai, saboda haɗin gwiwar jami’an tsaro gaba ɗaya da masu kwangilar tsaro na masu zaman kansu (TANTITA), tare da haɗin gwiwar Hukumar, an rage wannan da kashi 90 cikin ɗari zuwa ganga 9,600 a rana a watan Satumba 2025.

Bugu da ƙari, wasu dokoki guda biyu da hukumar ta gabatar a matsayin farko sun kuma taimaka wajen samun nasara: Dokar Auna Haƙar Mai na Sama teku (Upstream Measurement Regulation) da Dokar Bayyanar Jirgin Kaya na Ci gaba, waɗanda kowanne ya taka rawa a matsayin matakin farko wajen tabbatar da gaskiya a lissafin makamashi.

Ci Gaban Man Fetur 306 Tsakanin 2022 Zuwa 2025: A cikin aikin da hukumar ke da shi na haɓaka albarkatun mai na ƙasar, an samu rijistar ramuka 306 na ci gaban man fetur da aka haƙo kuma aka kammala tsakanin shekarar 2022 zuwa 2025.

Cire Ƙalubale Ga Binciken Mai Ta Amfani Da Bayanan Seismic Na 2D Da 3D: Hukumar NUPRC ta bayar da lasisin binciken mai ( PEL) na farko a Nijeriya don gudanar da babban binciken ƙasa da ruwa, wanda ya rufe km² 56,000 na bayanan seismic na 3D da bayanan nauyi (graɓity data).

Bugu da ƙari, Hukumar ta sake sarrafa km-layuka 17,000 na bayanan seismic na 2D da km² 28,000 na bayanan seismic na 3D, inda aka samar da hotuna masu ƙarfi da ƙuduri mai girma na tsarin man fetur, tare da rage rashin tabbas da da can ke hana yanke shawara wajen bincike.

Sauran tarin bayanai sun haɗa da km² 11,300 na sabon bayanan 3D da aka sarrafa zuwa PSDM, da kuma km² 80,000 na bayanan multi-beam echo sounding & seafloor geochemical coring.

Bayyana Rabon Lasisi: An sauya tsarin bayar da lasisi zuwa tsarin dijital cikakke da gaskiya, wanda NEITI ta yaba da shi kuma shugabancin ƙasa ya amince da shi, alamar babban ci gaba a sahihanci da kyakkyawan shugabanci.

Inganta amfani da kadarori: An aiwatar da manufar “Haƙowa ko Barin Filin” (Drill or Drop) don sake karɓar filayen da ba a aiki da su, wanda ya hanzarta bincike da haɓaka darajar kadarori.

Sabon Sahihin bincike: Ƙari mai ma’ana a aikin rig yana nuna sabuwar amincewar masu zuba jari da yanayi mai dacewa ga ci gaban makamashi cikin hankali.

Raba Hannun Jari Na Dabaru: Sauye-sauyen manyan fayilolin hannun jari masu daraja biliyoyin Dala don mayar da hankali kan haɓakar filayen mai na zurfin teku da kuma sabunta fayilolin kadarori.

Tsarin doka da ƙa’ida: Haɓakawa da wallafa wa dokoki masu hangen nesa don samar da bayyananniyar hanya, tabbacin aiki, da yanayi mai jawo jari.

Rage fashewar iskar gas (Gas flaring): Kammala Shirin Kasuwancin Fashewar Iskar Gas na Nijeriya, wanda ke haɓaka ɗorewar muhalli da kuma buɗe babbar damar jarin hannun jari.

Ci Gaban Al’ummomin Da Basu Masauki: Bayar da manyan kuɗaɗen tallafi ga amintattun ƙungiyoyin ci gaban al’ummomin masauki da amfani da kayan aikin shugabanci da suka dace da ESG kamar ‘HostComply,’ yana tallafa wa ɗaruruwan ayyukan al’umma da kuma ba da gudunmawa ga tsaro da ci gaban zamantakewa.

Sauyin Dijital: Cikakken sarrafa aikin dokoki ta hanyar dijital, rage tsangwama da ƙara ingancin bayar da sabis ga masu ruwa da tsaki a masana’antu da kuma jama’a.

Jagorancin Yankin: Jagoranci wajen kafa AFRIPERF, yana haɓaka daidaiton dokoki da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka a harkar mai da iskar gas.

Jagorancin Injiniya Gbenga Komolafe ya wuce kawai gudanar da harkokin doka; yana ɗauke da hangen nesa na dabarun ci gaban makamashin Nijeriya, wanda ke haɗa arzikin albarkatun ƙasa da ci gaban mai ɗorewa, amincewar masu zuba jari, da ci gaban al’umma.

Ayyukansa sun ƙarfafa suna da matsayin Nijeriya a matsayin ƙasa mai gaskiya, mai shirye-shiryen jawo jarin hannun jari a ɓangaren tekun ta sama, da kuma amintacciyar dandalin haɗin gwiwar makamashi na yankin.

A matsayinsa na abokin aiki a Ƙungiyar Injiniyoyin Nijeriya (FNSE) kuma Jami’in Odar Jamhuriyar Tarayya (OFR), Injiniya Komolafe ya bayyana haɗin ƙwazo da ƙirƙire-ƙirƙire. Ayyukansa na sana’a sun kasance kamar wani kiɗan symphony na shugabanci, inda kowace rawa ke haɗuwa cikin sauti mai daidaito wanda ke nuna ci gaba, juriya, da hangen nesa.

A cikin muƙamai daban-daban kamar Shugaban Gudanarwa na farko (pioneer managing director), Kamfanin Bututun Man Fetur da Ajiya na Nijeriya (NPSC) na NNPC; Babban Manaja na Rukuni, Ayyuka na Musamman, NNPC; Babban Manaja na Rukuni, Sashen Kasuwancin Man Fetur (COMD) na NNPC; Daraktan Zartarwa, Kasuwanci, Kamfanin Bututun Man Fetur da Kasuwancin Kayayyaki (PPMC) na NNPC; Babban Manaja, Ayyuka, Asusun Daidaita Farashin Man Fetur (PEF); da Babban Manaja, Ayyuka, Hukumar Kula da Farashin Kayayyakin Mai (PPPRA), ya kasance kamar bugun ganga mai ɗorewa wanda ke alkinta ƙirƙire-ƙirƙire, haɗin gwiwa, da ƙarfafa shugabannin gobe.

Baya ga rawar da yake takawa, shi mai daraja ne wanda gudunmawarsa ta samu karɓuwa a faɗin ƙasa da ma ƙetare. A matsayin Jami’in Odar Jamhuriyar Tarayya (OFR), ƙasar kanta ta yaba da sadaukarwarsa ta rayuwa. Jami’ar Benin ta ba shi digirin na girmamawa a fannin Kimiyya (D.Sc).

Ba wai ƙwararren fasaha ne kawai ba, Injiniya Komolafe mai samar da cigaba ne, yana haɗa gaskiya, amana da ɗan’Adam. Ya zauna a teburin kwamitocin shugaban ƙasa, inda muryarsa ke zama kiran gaskiya, da ɗabi’a mai kyau, da ci gaban ɗorewa.

A cikin fagen mai da iskar gas, ya ɗauki fitilar ƙirƙire-ƙirƙire, yana shimfiɗa dogwayen lamura masu tasiri a kan manufofi, hanyoyin aiki da haɗin gwiwa.

Injiniya Komolafe mutum ne mai kula da iyali, wanda ya yi aure cikin farin ciki kuma yana da ‘ya’ya. Yana jin daɗin wasan golf da kiɗa.

Domin jajircewa mai ban mamaki, nasarorin sauyi da jagoranci mai hangen nesa, Injiniya Gbenga Komolafe ya cancanci a ambace shi a matsayin GARZON SHUGABAN KAMFANI NA SHEKARA 2025. Shi haaiaa ne mai tsara makomar makamashin Nijeriya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu
Manyan Labarai

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin
Manyan Labarai

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Next Post
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025
Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

October 25, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.