Daga Bilkisu Yusuf Ali
Cigaba daga ranar 2 ga Maris, 2021
Kana da shaawar sake tsayawa takara a gaba?
Kin san dan siyasa kamar tsohon soja ne , yanzu tsohon soja a ce yana kwance anan ba shi da lafiya idan ya ji sarewa irin ta sojoji sai ya kasa ko motsawa? In kina wajen kya rantse motsawar da zai yi zai tafi filin daga ne.To haka yake ga dan siyasa in dai zangon takara ya zo ki ka ga dan siyasa bai motsi ba to ruwa ya daki babban zakara ya yi jagab fukafukin sun nutse. Duk wanda ya taba yin takara ba ya cewa ba zai yi takara ba sai dai kawai a bar wa lokaci a ga abin da lokaci zai zo da shi. Saboda haka sai mu yi fatan Allah ya kai mu lafiya mu ga abin da Allah zai yi.
A siyasance wanne mutum ka ke gani ya zame maka abin koyi?
Duk da dai na farfadi shigen irin wannan a cikin maganganu na amma jagora abin koyi a siyasa ai malam Ibrahim Shekarau ne.
To, za ka iya fadin irin gudunmawar da ka ba shi?
Muna tare da Malam Ibrahim Shekarau kuma mun ba shi gudunmawa tun kafin ya ci zabe da bayan ya ci zaben malam mutum ne mai son addini da koyi da shi kowa zai yarda da hakan in muka yi laakari da yadda daga lokacin da aka rantsar da shi a shekarar 2004 ya assasa duk ranar daya ga watan Almuharram ta zama ranar hutu sannan kuma aka kaddamar da kalandar muslunci ta farko shi ya kawo kaidar in har za a sa kwanan watan boko to sai an sa na muslunci . Don haka sai na yi tunani na ga ya za a kawo sauki da daidaito a wannan kwanan watan tunda maaikatun gwamnati suna da tsarin buga stamp.
A karshe idan za a samu irin wannan ‘stamp’ din da ke da baki biyu shi ne dai-dai da kudirin malam shekarau saboda haka na dinga yawo daga wannan kasa zuwa wannan kasa Ina neman ina ne ake da stamp mai baki biyu to saina samu a Germany to sai dai su baki biyun rubutun garinsu ne ba na boko ba ne to amma tunda ni muradina ya zama yana da Baki biyu sai na aika musu na ce ina so baki daya ya zama na boko baki daya ya zama na muslunci duk da na Gemany din ya yi tsada sai na koma China nan na samo shi kuma na kawo wa malam na ce gudummawar Kanawa ce mazauna Abuja. Malam ya yi murna sosai sannan na ce sai a nemi wanda zai je ya kawo shi. Sai malam ya ce ai to kai ya kamata ka kawo tunda kai ka kawo sample. Sai na ce to ai ni ba dan kwangila ne ba sai malam shekarau ya ce min ka zama dan kwangila yau saboda ana bukatarsu da yawa za a raba a ofisoshi” Yana dai daga cikin gudunmawar da muka bayar tunda shi mai son a raya adabi ne sai muka fito da tsarin su waye al’umma wadanda suka yi wa al’umma hidima don Allah ba don siyasa ba , sai dan raya al’umma ko ta bangaren ilimi Ko ta bangaren adabi ko ta bangaren sana’a ko dai ta wani abu na raya alumma.Sai muka kafa muhammadu Rumfa aword for women debelopment muka sa committee na manyan mutane akwai su Abdulkadir Sabo Tofa da manyan farfesoshi da manyan mutane Sannan muka yi yekuwa a Kano kan a kawo mana duk wani wanda ya ba da gudunmawa a Kano da bayanansa sai wannan committee su tantance su sannan sai a ba su lambar girmamawa. Saboda karamci irin na Sardauna shi yake ba da award din amma da sunanmu tunda mu muka assasa tsarin. Ba na mantawa akwai wata mata anan unguwar diso Ita ce mace ta farko da ta fara yin labarai a kafar rediyo, da aka fito da ita sai ta ce ita ta dauka ma an manta da ita. Sannan akwai wani wanda shi ya fara kirkiro yaki da jahilci anan Shahuci da sauransu . Wannan tsarin ya taimaki gwamnatin Malam kwarai da gaske.
Ko bayan n afito daga majalissa PDP ta kwace mulkin sai abin yazo dai-dai da gwamna ya kafa sabuwar doka kan kudin shiga ita kuma sabuwar dokar an ce shugaban wannan ya zama sai chief accounter to acikin Gwamnatin Babu sai aka fita nema to a cikin neman ne sai aka samo wani amma kuma shi dan Jigawa ne mazaunin Kano sai majalisa ta ce a’a ba za a sa wanda ba dan asalin garin Kano ba. Sai shugaban majalisa yace “to ai Kuna da danku yana Abuja tare muke da shi a hukumar tantance kudi ta Najeriya To haka na yi chairman na wannan board din. Kuma Alhamdulillahi Allah ya sa an cimma bukatu manya- manya na alumma da tsantseni da kuma kawo wa jiha cigaba. Saboda na farko an ce gidan yana daya daga cikin gidaje ukun da aka ce sun fi kowa karbar cin hanci da rashawa, wato da ‘Rebenue Board’ da ‘Land and Surbey da KASEPA kafin ta zama Knupda kuma Allah ya sa zamana aka samu warakar wannan. Na biyu harajin da ake tarawa bai kai wa miliyan daya a shekara amma ban shekara ba sai da ya zama Ina hada haraji sama da biliyan daya a wata.
Na uku an yi cuwa-cuwar ma’aikata aiki dan son rai kawai yanzu ka na ‘lebel 9’ ita tana lebel 12 kawai sai a ce tana karkashinki. Saboda haka ma’aikata suka ce aikin ba dadi. Sannan ke kadai sai a dankara miki aiki na mutum biyar saboda duk aikin na mutum biyar din akwai cuwa -cuwa kuma ke ake so saboda haka sai a tattara aikin a wajen ki ita kuma gata nan an kyale ta babu aikin a hannunta. Sannan mutane ba sa zuwa hutu akwai wanda ya shekara goma sha biyar bai taba zuwa hutu ba saboda tsoron kada ya tafi kafin ya dawo a dora wani.
Saboda haka da na zo sai na ce duk wanda ya shekara biyar sai ya matsa na yi canjin aiki na juya su shifing na sa a debo min file na zo gida na yi zaman dirshan na karance file din kowa kama daga shekarunka na aiki da ilimin da ka ke da shi. Shekara goma da na bar Rebenue har gobe idan mutum ya yi aiki a lokacin yana mutunta ni. Wannan gudunmawace da na bai wa Malam Shekarau aka ciyar da Rabanu gaba aka nuna kwarewa a cikin aiki da makamantansu. Ko bayan Malam Shekarau ya zama minista a jamiyyar PDP muna tare kuma ina da mukami a karkashinsa sannan a yanzu da yake sanata Ina nan dai a tare da shi.
A lokacin da Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ya nada shi Sardaunan Kano akwai wasu littatafai da na buga Wanda ya shafi sarautar kuma akwai wasu fastoci da na bugo a Abuja wani yace tunda aka likata har yau tana nan babu abin da ya same ta. Ni Ina rokon Allah subhanahu wata ala Mai kowa Mai komai Ina so ya nuna min aya kamar yadda ya nuna min a Abuja, ya sake nuna min aya Kano. Ko ma wane mukami ne muna rokon Allah Mai kowa Mai komai da nuna mana aya.
Ya makomar kungiyar yan Kano mazauna Abuja take a yanzu?
Ni tunda na bar kungiyar Kanawa mazauna Abuja suka bai wa wani sun dauka kudi nake samu a hannun gwamna ba su san kishi ne da jajircewa ba gashinan dai haka suka bar kungiyar ta fadi
Mene ne burinka?
Burina shine Kano ta bunkasa ta cigaba da rike kambunta na uwa ga duk Najeriya. Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya da arziki mai dorewa Allah ya sa mu cika da kyau da imani mu tashi da shi.