Gyara Sakandiren Chibok: ‘Yan Majalisa Na Neman Bayanin Yadda Aka Kashe Naira Miliyan 500

Ndume

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

 

Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar kudancin jihar Borno a zauren majalisar dattawa, tare da Hon. Ahmed Jaha mai wakiltar kananan hukumomin Chibok, Damboa da Gwoza a zauren majalisar wakilai daga jihar, sun bukaci cikakken bayani dangane da yadda aka kashe naira miliyan 500 da aka ware domin sake gina sakandiren Chibok.

 

Wadannan yan majalisar tarayya daga jihar Borno sun yi wannan kiran ne ranar Talata a garin Chibok, a sa’ilin da suke tattaunawa da manema labarai dangane da kaddamar da aikin ginin makarantar sakandiren garin: ‘Gobernment Seconday School’ (GSS) wanda gwamnatin jihar Borno ta aiwatar ranar Litinin.

 

A hannu guda, sun ce yin bayanin filla-filla ya zama dole domin warware zare da abawa wajen gano abinda ya faru da kwangilar naira miliyan 500 da aka bayar don sake gina makarantar, a karkashin shirin: ‘Sabe School Initiatibe’ tun a 2015, wanda abu mai daure kai, shi ne ta ya gwamnatin tarayya zata kasa kammala wannan aikin, har sai daga baya a lokacin da Gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci makarantar a cikin watan Nuwamban 2020, sannan ya bayar da umurnin sake gyara makarantar baki daya.

 

Har wala yau, makarantar wadda gwamnatin jihar Borno ta gyara don ci gaba da ayyukan koyarwa, wadda Ministar kula da harkokin mata- Misis Pauline Tallen ce ta kaddamar da ita ranar wannan Litinin da ta gabata.

 

Har wala yau, Sanata Ndume ya shaidar da cewa tambayoyin da ya kamata a bayar da amsarsu sune, ya aka yi da wadannan kudin da gwamnatin tarayya ta ware, wanda daga bisani kuma ta nemi daukin jihar Borno wajen ci gaba da kammala aikin.

 

“A lokacin guda muna jinjina wa Gwamna Zulum bisa kokarin sake gina wannan makaranta, a bangare guda kuma muna da bukatar a bayyana mana yadda aka yi da kudaden da aka ware domin wannan aikin, shi ne halin da ake ciki tun kafin a mika wa gwamnatin Borno ci gaban aikin.”

 

“Sannan a nawa binciken da na gudanar, na gano an narka makudan kudin da suka zarta aikin da aka gudanar a kasa, nesa ba kusa ba kafin gwamnatin jihar Borno ta karbi ragamar ci gaba da aikin.”

 

“Haka zalika kuma, ina da masaniyar cewa majalisar wakilai ta kafa kwamitin da zai binciki yadda aka aiwatar da kudaden a karkashin ‘Sabe School Initiatibe’, kuma ina bayar da goyon baya dangane da wannan yunkuri.” in ji Ndume.

 

A nashi bangaren, dan majalisar wakilai ta tarayya, Hon. Ahmed Jaha wanda shi ne shugaban karamin kwamitin wanda aka damka wa alhakin bincike dangane da aikin ginin sakandiren Chibok, ya ce kwamitin zai yi aiki wajen zakulo yadda aka yi da kudaden da aka ware don sake gina makarantar tare da gano shin ko an aiwatar da kudin bisa ga manufar da aka ware su?

 

Hon. Jaha ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Borno na sake gina makarantar wadda ya mayar da ita cikin hayyacinta tare da ci gaba da gudanar da karatu, kamar yadda Gwamnan ya dauki alkawari kuma ya cika.

Exit mobile version