Kasidu biyu masu taken, Matsalar Wutar Lantarki;
Yadda Wayoyin Wuta Suka Harharde, da kuma Wutar Lantarki: Badakala da Cin Zalin ‘yan Nijeriya, sun yi nuni ne da yadda aka yi wa Nijeriya zagon kasa a rana daya, aka wargaza da kuma tarwatsa NEPA/PHCN, aka kuma kasafta su, aka yi warwason su da sunan inganta samar da wutar lantarki isasshe kuma ingantance.
A yayin da daya bangaren ya yi karin haske kan makudan kudade da suka sulale cikin harkar wutar lantarki daga wasu hanyoyin da suka shafi gwamnati. Wutar lantarki da ake samarwa wacce ba ta kai ga mabukata ba ko ga masu amfani da ita ba da sauran batutuwa masu daure kai da suka shafi karar ma’aikata da hakkinsu inda kuma ya haska batun rashin bin diddigi da rashin inganci da kwadayin wadanda aka dauka aiki dmin su tabbatar da samar da wadatacciyar wutar lantarki.
Wannan shi ne cikamakn fadakarwa tawa ga hukumomi da sauran masu kishin Nijeriya da ‘yan Nijeriya.
‘Yan damfara da zamba a lunguna da sako a ko’ina
Kasafin kudin shekara-shekara da ake ware wa bangaren wutar lantarkin Nijeriya na tsawon shekaru da dama, ya yi nuni da cewa gwamnati a RIKICE take, kuma tana da hannu dumu-dumu cikin badakalar da ake tafkawa a Nijeriya da kuma kan ‘yan Nijeriya. A maimakon a shawo kan lamarin abin sai kara ta’azzara yake yi.
A nan ga takaitaccen adadin kudin da aka kashe da kuma tambayyi masu mahimmanci, ‘Shin zambar da ake tafkawa bai isa bane a kan Nijeriya da ‘yan Nijeriya?’
An samar da kudade kamar haka daga shekarun 2015 (Naira biliyan 214.93), 2016 (Naira biliyan 273.32), 2017 (Naira biliyan 236.47), 2018 (Naira biliyan 264.08), 2019 (Naira biliyan 256.97), 2020 (Naira biliyan 266.02), 2023 (Naira biliyan 239), da 2024 (Naira biliyan 344). Wadannan alkaluma ne a cikin kasafin kudin shekaru daban-daban da suka shude.
Babban abin da ya fi muni shi ne, akwai abin da ake kira ‘Unpaid Capacity Charges’ Wadannan basussuka ne da GENCs ke bin hukumar saye da sayar war lantarki mai suna, ‘Nigeria Bulk Electricity Trading’ (NBET) Plc. Wannan yana da alaka da abin da ake kira ‘Wahalar Kawar da Karfin Wuta ta hanyar manyan layukan wuta’ wato ‘Difficulty to Evacuate Available Generating Capacity’ a turance.
Wannan batu ya fito fili ta bakin kungiyar Kamfannin Samar da Wutar Lantarki (APGC), kuma wannan cajin yana kunshe ne a cikin Yarjejeniyar Sayen Wutar Lantarki (Pwer Purchase Agreements -PPA).
To ga wasu alkaluman wasu shekaru kamar haka; Naira biliyan 214.9 a shekarar 2015; Naira biliyan 273.3, a shekarar 2016; Naira biliyan 236.4 a shekarar 2017; Naira biliyan 264.08 a 2018, da Naira biliyan 256.9, Naira biliyan 266.01 da Naira biliyan 120.2 a 2019,2020 da 2021 bi da bi. Kodayake NBET ba ta yi na’am da alkaluman ba amma ta ce kuma ba duka GENCs ne ke da hakki ba a cikin wadan nan kudade. Tambaya, idan ba rami mai ya kawo maganar rami?
Tashin hankali kan kwatankwacin karfin wutar lantarki
Shin GENCs da DISCOs, suna iya cika alkawari da yargejeniyar da suka shi ga lokacin da suka yi wa NEPA warwas kuwa? Amsa a nan ita ce a’a.! Ina Mafita?
Na farko, Tsarin shinge na Banding da kuma karin kudin wutar lantaki ga wadanda suke kan Band A wato Tariff Rate Hike na baya-bayan nan, tsarin WARIYAR LAUNIN FATA ne kawai da kuma ZAMBA da ake nufi don tabbatar da rashin adalci wajen rarraba rashin isasshiyar wutar lantarki ta hanyar isar da shi ga masu gata kawai.
Shin NBET za ta iya gwajin karfin wuta da ake samar wa daga GENCs? wannan abu ne mai wahala.
Wannan samar da makamashi na awa 24, daga ina zai fit? Hakika, daga sauran feeders a kan band B zuwa E, ma’ana mutanen da suke kan wannan band za su kasance kullum ba tare da isasshiyar wutar lantarki ba.
Yanzu idan aka ce ba za a samar da wutar lantarki na awanni 24 ba, yayin da wadanda ke da mitoci suka riga su ka sayi wutar lantarki a kan haka, me zai faru da kudin na su?
Kuma masana’antun da ke kan band A, za su kara farashin kayayyakinsu da ayyukansu kai tsaye k kuwa?
Abu na biyu, abubuwan da ke tattare da jimlar adadin da abkan ciniki za su biya, su ne Cajin Sabis, Cajin Makamashi, Kafaffen Cajin, Cajin na Lkacin-Amfani (TU), da Cajin Blck. A wannan kimar, abubuwa nawa ne za a gabatar kuma a kara su nan ba da jimawa ba?
Na uku, NERC ta amince da karin farashin mitcin lantarki da aka riga aka biya tun daga watan Satumbar 2023, inda mita mai layi daya ya tashi zuwa NGN81,975.16 da kuma mita mai layi uku ya tashi zuwa NGN143,836.10. Wannan ya yi daidai da kama da masu sayar da ‘garri’ su sanar da kwastomominsu cewa dole ne su da ‘mudu’ kafin su samu damar sayen garri.
Na hudu, me ya sa NERC za ta amince da karuwar nan take a ranar 1 ga Afrilu 2024 a cikin jadawalin wutar lantarki ba tare da duk tsarin da ake bukata ba, kamar kafa tashar intanet.?
Na biyar, a karkashin tsare-tsare kamar tsarin samar da kadarrin Mita (MAP) da kuma ‘National Mass Metering Prgramme’ (NMMP), an samar da kudade dn samar da mitoci kyauta ga masu amfani ta hanyar lamuni daga CBN zuwa DISCs. Ya zuwa yanzu, abokan ciniki nawa ne suka ji dadin wannan karamcin?
Na shida, dokar samar da wutar lantarki da aka amince da ita ta zo da wasu hukunce-hukunce masu muni irin na shekaru uku na satar wutar lantarki, yayin da yanke wuta ba bisa ka’ida ba ya jawo cin kanfanin wuta tarar Naira 2,000 kacal!
Na bakwai, tabbas DISCs da GENCs ba su cika dukkan Sharuddan Sayarwa ba, sabda haka, yaushe NERC za ta fara cin su tarar NGN20m kowace rana?
Na takwas, menene hukuncin DISCs wadanda ke jinkirta samar da ‘Tamper Cde’ ga abokan cinikinsu wanda ke haifar da asarar kudaden shiga da dai sauransu ga daidaikun mutane da kamfanni?
Na tara, Ministan wuta lantarki ya bayyana ‘cewa taron zai yi la’akari da sanya hukuncin kisa ga masu amfani da wutar lantarki da suka ketare mitoci da satar wutar lantarki, da kuma wadanda ke lalata kaddarorin wutar lantarki.’ To wanne hukunci ne zai fada akan wadanda suka ha’inci ‘Yan Nijeriya da Nijeriya ta hanyar yin gwanjon kaddarorin wutar lantarki na kasa?
Na goma, game da wariyar launin fata, mene zai faru idan abokin ciniki yana son a ba shi wutar lantarki na awanni 24? Sabda yana nufin DISCs na iya samar da wutar lantarki na awanni 24 amma sun zabi kada su ba da?
Na goma sha daya, tare da bayar da lasisi ga masu gudanar da aikin rarraba wutar lantarki masu zaman kansu guda 17, wadanda 11 ke aiki a halin yanzu, shin suma za su shiga cikin wani shiri na CBN mai iya gabatarwa a fannin wutar lantarki kuma a wane tsari? Kuma wane babban layin wuta (grid) ne zai ciyar da su?
Na gma sha biyu, yaushe ne za a dakatar da kiyasin lissafin ga kwastomomin da ba su da mitocin bisa la’akari da duk kudin da aka yi amfani da su don samar da mita da gwamnati ta riga ta biya?
Na goma sha uku, me ya sa dokar samar da wutar lantarki da aka amince da ita ba ta bayar da hukuncin kisa ga DISCs na kin inganta injina don tabbatar da sahihancin lissafin kudi da rage dokar da kiyasin yin lissafin kudi da zamba a kan ‘yan Nijeriya?
Na goma sha hudu, alhakin waye idan aka samu ‘Lad Rejectin’ da kuma ‘Lad Dumping’?
Na goma sha biyar, me ya sa za a ci gaba da samar da kudade ga harkar makamashi mai yawa wanda ba ya isa ga abokan ciniki, da ci gaba da samar da makamashi tare da watsawa da sanin babban layin watsa wuta basu cikin hayyacinsu ba kuma za su iya daukar duk wutan ba.
Na sha shida, laifin wane ne rashin isassun na’urorin da ake watsawa ko kuma na’urar watsawa (Transmissin Substatins ran Injectin Substatin).?
Na sha bakwai, laifin wane ne ba a samar da Kadi ba wata (Spinning Reserbe)?
Na sha takwas, yaushe NERC ko Ma’aikatar Wutar Lantarki za su gurfanar da GENCs da DISCs a kan karya duk sharuddan gwanjo da aka yi wa NEPA ko babu ne?
Kwatsam a dauke wutar lantarki
Duk wasu dalilai marasa kan gado da aka bayar na wargaza NEPA sun wargaje.
Dukkan sharuddai da yarjejeniyyin gwanjn NEPA an karya su. Duk dukkan kasa, an tattake su yayin da aka yi wa Kundin Tsarin Mulki karan tsaye.
Ministan Wutar Lantarki, a wajen bikin bude wani taron samar da wutar lantarki na Nijeriya (NESI) na kwanaki uku indan mahalarta, da sabbin shiga kasuwar wutar lantarki da masu ruwa da tsaki, (NMPSR) suka hallarta, ya bayyana, a takaice cewa, “Mafi yawan kasashe ba su wargaza da kuma tarwatsa harka wutar lantarkin su ba, amma mu a nan Nijeriya mun yi wannan aika-aikar’.’
A karshe, yaushe ne lokacin da ya dace a warware wannan ko gurfanar da wadanda suka yi FYADE da kuma GARKUWA da harkar wutar lantarki a Nijeriya?