Fata na da matukar muhimmancin ga Kowanne dan’Adam ya zama mai gyara jiki tare da tsaftace shi, musamman ga ‘ya mace, shima namiji ba a ce kada ya gyara jiki ba, amma dai an fi bukatar mace ta zama mai kulawa da gyaran jikinta da kuma tsaftace shi a koda yaushe, musamman ga matar da ke gidan aure.
Domin shi fa zaman aure ba zai yiwU ba ga ‘ya mace ba tare da gyaran jiki da kulawa da tsaftarsa ba, koda kuwa mijinki ba mai kula da gyaran jikin bane, to ke a matsayinki na ‘ya mace ki yi kokari ta hanyar kissa da dabaru namu na mata ki sa shi ya rinka gyara jikinsa ke ko ke da kanki ma za ki iya gyara misa.
- Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz
- Ta Yaya Kasashe Masu Tasowa Za Su Iya Tinkarar Yakin Haraji Da Amurka Ta Tayar?
Sau da yawa za ki ga gidajen ma’aurata mace daga gidan iyayenta ta taho da tarbiyya ta gyaran jiki da tsabtace shi amma idan ta zo gidan aure ta hadu da namiji da bai damu da gyara ba sai ta ajiye ta dauki dabi’arsa ta ko in kula, shi ne sai ki ga gida ya hadu ya cakude idan an haifi yara suma duk su tashi a haka.
Gyaran jiki:
Wasu gidajen aure kuwa sai ka samu mijin mai tsananin gyaran jiki da kulawa har ka ga ya tsaya bata lokaci yana gyara fuska da fatar jiki ke in kika gashin sai ki rantse mace ce ba namiji ba, saboda yadda fatarsa ke kyalli da haske, amma idan ka shiga gidansa sai ka tarar da matarsa tamkar mai aikin gidansa ita ma wacce ba ta damu da gyaran jiki ba.
Don haka yana da matukar muhimmancin ga kowanne dan Adam ya lazamta wajen gyaran jikinsa, mace ko namiji musamman ma ga ma’aurata.
Za Mu Ci Gaba Mako Zuwa Idan Allah
Ya Kai mu
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp