Majalisar wakilan Nijeriya ta bayyana cewa tana da kwarin giwa kan mataimakin shugaban majalisa, Rt. Hon. Benjamin Kalu, zai sauke nauyin da aka dora masa na shugabancin kwamitin gyaran kundin tsarin mulki, wanda ba za su taba cin amanan ‘yan Nijeriya ba.
A kwanan nan ne majalisar ta kafa kwamiti da zai duba shawarwari na canje-canje da gyare-gyare na kundin tsarin mulki na shekarar 1999, inda aka dora shugabancin kwamitin ga Kalu tare da wasu kwararrun ‘yan majalisa a matsayin mambobi.
- Ku Je Ku Magance Matsalar Yunwa Da Ta Addabi Jama’a -Fintiri
- Babu Inda Na Ce Na Fi ‘Yan Nijeriya Shan Wahalar Tsadar Rayuwa -Ɗangote
Wannan kwamiti shi ne na shida da aka kafa tun a shekarar 1999, domin sake duba kundin tsarin mulki da ake amfani da shi a yanzu, ana tsammanin za a kaddamar da shi a ranar 26 ga Fabrairun 2024.
Da yake yi wa ‘yan jarida karin haske a Jihar Kano, mai magana da yawun mataimakin shugaban majalisar wakilai, Hon. Philip Agbese ya bayyana cewa ‘yan majalisa suna da kwarin gwiwa a kan mataimakin shugaban majalisar wakilai, kuwa kwamitinsa zai yi aikin da aka dora masa kan lokaci.
Ya ce, “Tun lokaci mai tsawo majalisar kasa take yunkurin sake fasalin kundin tsarin mulki na shekarar 1999, tare da niyyar sauya wasu daga cikin dokokin ta yadda za su dace da zamani. A wasu lokutan, majalisa na samun nasara, amma kuma a wani sa’ilin kwamitin majalisa yakan gaza yin aikinsa.
“Amma wannan kwamitin da aka danka wa Rt. Hon. Benjamin Kalu zai samu nasarar yin aikin gyara kundin tsarin mulkin kasar nan. Ya kamata ‘yan Nijeriya su kwantar da hankalinsu a rana daya komai zai iya sauyawa.
“Wannan kwamitin zai yi amfani da shawarwarin mutane da mabambantan masu ruwa da tsaki da kungiyoyin fararen hula da ma’aikatun gwamnati da masarautun gargajiya da kungiyoyin mata da kuma ‘yan kasuwa masu zaman kansu wadanda suke taimakawa wajen bunkasa tattalin arziki, domin samun nasarar gyarar kundin tsarin mulkin Nijeriya.”
Haka kuma Hon. Agbese ya bayyana cewa wannan lokaci ne da kungiyoyi da ma’aikatun gwamnati za su samu dama na sauya wasu daga cikin dokokin tsarin mulki na 1999, domin yin aiki kafada da kafada da wakilansu a lokacin da kwamitin ya fara aiki a hukumanci a kasrshen wannan wata.
“Akwai kudurorin doka guda 40 da majalisa ke neman a saka su a cikin tsarin mulki. Wasu daga ciki za su kawo karshen matsalolin jinsi da masarautun gargajiya da bai wa kananan hukumomin ‘yancin gashin kai da matsalolin kudade da dai sauransu.
“Kwamitin zai tabbatar ya kammala aikinsa a watan Disambar 2025. Ina kira ga masu ruwa da tsaki da su yi aiki kafada da kafada da wakilolinsu da kwamitin saboda a kammala aikin kan lokaci.”
Mataimakin shugaban majalisar wakilai kuma shugaban kwamitin gyaran kundin tsarin mulki ya gana da dukkan mambobin kwamitin a ranar Laraba da ta gabata, inda ya yi alkawarin cewa kwamitin zai kammala aikinsa a watan Disambar 2025.
Kalu ya bukaci mambobin kwamitin da su shirya yin aiki tukuru saboda samun damar yi sauye-sauye na kundin tsarin mulki kan lokaci kamar yadda suka yi wa ‘yan Nijeriya alkawari.