Kwamitin Majalisar Dattawa kan gyaran kundin tsarin mulki na 1999, ya shirin gudanar da taron sauraron jin ra’ayoyin jama’a a wasu sassan Nijeriya na kwanaki biyu, domin tattara bayanai kan kiraye-kirayen kudirin gyara kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana a cikin wani sanarwa da aka fitar a Abuja, cewa sauraron jin ra’ayoyin al’umma zai gudana Legas (Kudu maso yamma), Inugu (Kudu maso gabas), Ikot Ekpene (Kudu maso yamma), Jos (Arewaci ta tsakiya), Maiduguri (Arewaci ta Gabas) da Kano (Arewaci ta yamma).
- Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Shaida Gamsuwa Da Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya
- Firaministan Singapore: Jama’ar Sin Suna Da Kwarewar Kirkire-Kirkiren Fasahohi
Kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar da ke dauke da sa hannun mai ba da shawara na musamman kan kafofin watsa labarai na mataimakin shugaban majalisar datta, Ismail Mudashir, sauraron jin ra’ayoyin zai gudana ne a ranakun 4 da 5 ga Yuli, 2025 a wurare daban-daban da aka tanada.
Sanarwar ta kara da cewa sauraron jin ra’ayoyin jama’a, zai binciki muhimman batutuwa na kasa nan, ciki har da ‘yancin bai wa kananan hukumomi da gyare-gyaren zabe da na bangaren shari’a da kirkirar jihohi da ‘yansandan jihohi da kuma manufofin gwamnati.
Daya daga cikin kudirorin da aka fayyace a cikin sanarwar, yana ba da shawarar kafa majalisin kananan hukumomi a matsayin mataki na uku na gwamnatin tarayya don tabbatar da kasancewarsu cikin dimokuradiyya da kuma tsawon wa’adin mulkinsu.
Bisa ga sanarwar, wannan wani sashe ne na sabon yunkuri na ba da cikakken ‘yanci ga majalisar kananan hukumomi 774 na kasar nan.
Haka kuma a kan gyaran kananan hukumomi, wata kudirin doka da ke neman kirkiro wata hukumar zabe mai zaman kanta ta kananan hukumomi (NALGEC), wanda za ta dunga shiryawa, gudanar da kuma kula da zaben kananan hukumomin, za a kuma gabatar da ita ga ‘yan Nijeriya don yin nazari a taron sauraron jin ra’ayoyin.
Wadansu batutuwa da aka fitar a cikin sanarwar da suka hada da kudirin dokoki guda biyu kan tsaro da manufar samar da ‘yansandan jihohi da majalisar tsaro na jihohi don tsara manufofin tsaro na cikin gida a matakin yankuna.
“A bangaren gyaran manufifin kudade kuwa, za a duba dokoki guda shida ciki har da dokar da za ta ba da iko ga hukumar rarraba haraji ta kasa don tilasta bin doka da rarraba kudaden haraji daga asusun gwamnatin tarayya da kuma inganta tsarin nazarin hanyar rarraba kudaden.
“A cikin wata sabuwar mataki tare da magance rashin daidaiton jinsi, kwamitin zai kuma yi nazarin wata doka da za ta samar da karin kujeru ga mata a cikin majalisun tarayya da majalisun jihohi.
“Don karfafa masarautun gargajiya, za a duba wani kudirin doka za sauya kundin tsarin mulki domin kafa majalisar masarautu gargajiya ta kasa da majalisar masarautun gargajiya ta jihohi da majalisar masarautun gargajiya ta kananan hukumomi.
“A kan gyaran tsarin zabe kuwa, za a tattauna wani shawarwari da ke neman gyara kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 don ba da damar tsayawa takara kai tsaye a kowane mataki na zabe, daga kananan hukumomi zuwa shugabancin kasa a taron sauraron jin ra’ayoyin.
“Jimlar wasu kudirorin doka fiye da 20 da ke neman gyara tsarin shari’a na kasar, ciki har da lokacin da ake zartar da hukunci da kuma fadada ikon kotunan zabe, suna daga cikin batutun da za a duba.
“Shawarwari guda talatin da daya kan kirkiro jihohi, suna cikin batutun da za a dubawa a taron sauraron jin ra’ayoyin.”
Kwamitin ya jaddada muhimmancin shigar jama’a wajen tsara kundin tsarin mulkin kasar, ya yi kira ga kowa da ya halarci taron sauraron jin ra’ayin jama’a na yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp