Erling Haaland da Phil Foden sun zira kwallaye uku-uku yayin da Manchester City ta lallasa Manchester United da ci 6-3.
Ayau Lahadi, maki daya ne tazara tsakanin masu jan ragamar gasar Premier, Arsenal dake da maki 21 da Manchester city na biyu dake da maki 20.
Haaland ya zura kwallaye uku sau Uku a cikin wasanni uku da suka buga a gida na gasar Premier inda ya ci kwallaye 17 a wasanni 10 da ya buga wa zakarun Ingila.