An gudanar da taron karawa juna sani na shekara-shekara karo na farko dangane da aikin koyar da harshen Sinanci a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, inda aka jaddada bukatar sa kaimi ga fadada koyar da harshen Sinanci a duk fadin kasar, wacce take gabashin Afirka.
Taron wanda ya hada malamai da masana harsuna na kasar Sin da ta Habasha, ya mayar da hankali kan kafa tsarin koyar da harshen Sinanci mai inganci a kasar Habasha, da tunkarar kalubalen da ake fuskanta wajen kafa wannan tsari.
Da yake jawabi a wajen taron, mashawarcin jakada na ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Habasha, Zhang Yawei, ya ce manufar taron ita ce musayar gogewa, da dorawa kan nasarorin da aka samu, da warware batutuwa, da kuma ciyar da aikin koyar da harshen Sinanci gaba a Habasha tare.
Kazalika, mataimakin shugaban ofishin ilimi na yankin Oromia, Bultosa Hirko, ya bayyana cewa, koyar da harshen Sinanci na samun karbuwa a kasar Habasha, da samar da dammamaki a fannin tattalin arziki, da sa kaimi ga musayar al’adu, da samar da hadin gwiwar moriyar juna a tsakanin kasashen biyu. (Yahaya)