Daga Ahmed Muh’d Danasabe,
Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu a wani mummunar hadarin mota daya auku a kauyen Irepeni dake kan babban hanyar Abuja zuwa Lokoja dake jihar Kogi, a ranan Talatar da ta gabata.
Rehotanni sun ce hadarin ya faru ne a tsakanin motoci biyu, wato bas kirar Toyota Hiase da kuma Ludurious Bas dauke da fasinjoji daga yankin kudu maso kudu zuwa arewacin Najeriya.
Kamandar rundunar kiyaye haddura ta kasa( FRSC), reshen jihar Kogi, Mista Solomon Agure ya tabbatar aukuwar lamarin ga wakilinmmu.
Agure ya ce, Motar Toyota Hiase din tana kan hanyarta ne ta zuwa Auchi da ke Jihar Edo a yayin da kuma Ludurious bas din ta taso daga yankin Okene.
Nan da nan, Ludurious bas din ta buge karamar motar ta Toyota Hiase inda nan take motar ta afka cikin daji kuma mutane 15 suka rasa rayukansu cikin motar nan take inda daga bisani mutum biyu suka rasu a asibiti.
Daga nan kamandan ta FRSC ya shawarci masu motocin hawa dasu rika rage gudu da kaucewa tafiyar dare tare da tsara yadda zasu rika yin balaguro domin kaucewa aukuwar hadarruka.” Yana da muhimmanci masu ababen hawa su rika bin ka’idojin tuki domin kaucewa hadurruka,” in ji Shi.
Agure ya ce, rundunar ta FRSC ta turo jami’anta 522 domin tabbatar da ganin ababen hawa sun samu sukuni da kuma kaucewa cunkoson motoci a lokacin bukukuwan kirsimati da sabuwar shekara.
Kamandan ta FRSC ya kuma kara da cewa rundunar zata karo jami’anta daga jihohin Ekiti da kwara domin tallafawa rundunar dake nan jihar Kogi domin ganin an gudanar da bukukuwan Kirsimati da sabuwar shekara cikin walwala da jin dadi.