Abubuwan Da Uwargida Za Ta Tanada:
Kwai, Albasa, Magi, Gishiri, kuri leda fara, alayyahu idan kinaso amma ba dole bane:
Yadda uwargida zaki hada Awarar Kwai:
Uwargida zaki samu kwanki kamar goda biyar zuwa sama ya danganta da yawan yadda kike so, za ki samu roba haka wadda za ki fasa kwain acikin ta sai ki fara fasa kwain kina zubawa aciki harki gama fasasu, bayan kingama fasawa sai ki gyara albasarki ki yayyanka ta kanana a cikin kwain sannan ki dansa magi kadan sai ki sa gishi da kuri idan kina so za ki iya jajjaga dan attaruhu kisa sai ki kadasu gaba dayan su tare da kwain bayan sun gaurayu so sai anan ne idan uwargida kina son alayyahu sai ki yayyanka shi kanana kanana ki zuba idan kuma ba kyaso sai ki bar shi ba sai kinsa ba, sannan ki daukko farar ledar ki sai ki fara zubawa a cikin ledar kamar yadda ake zuba alala haka za kina zubawa kina kullawa har ki gama sai ki samu tukunya kisa mata ruwa kamar yadda zaki dora alala sai ki debo wannan kwain da kika kukkulla shi a farar leda sai kisa a cikin ruwan tukunyar ki dakko tukunyar ki kunna wuta ki dorata ki rufe kibarta ta yi kamar minti goma zuwa shabiyar.
Daga nan sai ki duba ta idan tadahu za kiga ta kama jikin ta tasaki ledar ta zama guda daya a ciki idan kika ga ta yi haka sai ki sauke ta, bayan kin sauketa sai ki kwasheta a cikin tukunya kisata awata roba da ban ko tire saboda tadan huce sai ki sunce ledar ki zubeta a tire sannan ki yayyanka ta kamar yankan awara harki gama yayyanka su haka, sai ki zuba mai a abin suya ki dora shi a wuta ya yi zafi kisa masa ‘yar albada kadan saboda ya yi kamshi, sannan ki dakko wannan yangyaggyan kwain kina sawa a man da yake kan wutar har abin suyar ya cika sannan kibarta taci gaba da soyuwa, yadda zakigane ta soyu za ki ganta tayi kalar kasa kasa kuma kamshi yana tashi sai ki juya saman shima ya soyu. Wannan ita ce Awarar Kwai ba a bawa yaro mai kiuya.