Ministan harkokin wajen kasar Mali Abdoulaye Diop ya bayyanawa ’yan jarida a wata rubutacciyar zantawa a kwanakin baya cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Afirka da Sin, hadin gwiwa ce ta sada zumunta a tsakanin ’yan uwa.
Ya ce, tun bayan da aka kafa dandalin hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC, dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu ke bunkasa yadda ya kamata, yana kuma fatan za a ci gaba da inganta hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu bisa tunanin samun moriyar juna.
Minista Diop ya bayyana cewa, tun bayan kulla huldar diplomasiya tsakanin Mali da Sin shekaru 62 da suka gabata, dangantaka tsakaninsu ke ci gaba da bunkasa, tare da amfanawa jama’ar kasashen biyu.
Ya bayyana cewa, kasar Mali tana martaba manufar Sin daya tak a duniya, da kara yin mu’amala tsakanin manyan shugabanninsu. Yayin da kasar Mali take fuskantar yaduwar cutar COVID-19, kasar Sin ta sha ba ta gudummawar kayayyakin yaki da cutar, domin taimakawa kasar ta Mali wajen inganta karfinta na yaki da annobar. (Zainab Zhang)