Harkar ba da ilimi wadda masu iya magana kan ce gishirin zaman duniya, tana da matukar muhimmanci ga makomar kowacce al’umma.
A kwanan baya, an gudanar da taron karawa juna sani kan hadin gwiwar Sin da Afirka a bangaren aikin ilimi, a Addis Ababa na kasar Habasha, inda jami’an kungiyar tarayyar Afirka AU, da manyan kusoshi masu kula da aikin ilimi na kasashen Afirka, suka tattauna dabarun amfani da hadin gwiwar Afirka da Sin ta fuskar ilimi, wajen taimakawa kasashen Afirka cimma muradunsu na raya kasa, wato Ajandar shekarar 2063. Kana a nashi bangare, Mohammed Belhocine, kwamishina mai kula da aikin ilimi, da kimiyya da fasaha, da kirkiro sabbin fasahohi, na kungiyar AU, wanda ya halarci taron, ya yaba wa kasar Sin kan taimakon da ta ba kasashen Afirka wajen horar da kwararrun da suke bukata, a kokarinsu na raya tattalin aziki da zaman al’umma.
- Sin Ta Bayyana Takaici Game Da Yadda Kwamitin Tsaron MDD Ya Gaza Zartas Da Kudurin Tsaron Sararin Samaniya
- Sin Ta Sanya Wasu Karin Kamfanonin Amurka Cikin Jerin Kamfanonin Da Ba Za A Iya Dogaro Da Su Ba Bisa Sayarwa Taiwan Makamai
Hakika, ana ta samun karin sakamako masu armashi bisa hadin gwiwar da kasashen Afrika da kasar Sin suke yi ta fuskar aikin ilimi, cikin shekarun nan. Kamar dai yadda jakadan kasar Sin a kungiyar AU Mista Hu Chunhua ya yi bayani, tun daga shekarar 2012, kasar Sin ta kafa wani asusun raya aikin ilimi a karkashin kungiyar raya aikin ilimi, da kimiyya da fasaha, da al’adu, ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO), sa’an nan ta yi amfani da kudin asusun wajen horar da malamai dubu 10 na makarantu daban daban na kasashen Afirka. Ban da haka, Mista Hu ya ce a shekarun nan, a kan samu dalibai ‘yan kasashen Afirka fiye da dubu 50 da ke zuwa kasar Sin don karatu a duk shekara, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin ta riga ta zama wani wuri mai muhimmanci da matasan nahiyar Afirka ke son zuwa don neman karin ilimi.
Idan muka waiwayi abubuwan da suka faru a kasar Najeriya a kwanan baya, za mu iya ganin dimbin sakamakon hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin aikin ilimi. Misali, a ranar 17 ga wata, an yi wani biki a birnin Abuja, domin mika bangare na farko na jami’ar sufuri ta tarayyar Najeriya, da wani kamfanin kasar Sin ya zubawa jari, gami da daukar nauyin gina ta. Bikin ya nuna yadda za a fara aiki da jami’ar, wajen samar da kwararru a fannin aikin sufuri da kasar Najeriya ke bukata.
Ban da haka, a kwanan baya, an kaddamar da shirin hadin gwiwa na “hanyar siliki” a birnin Lagos, wanda ke da niyyar tura wasu hazikan dalibai na Najeriya zuwa kwalejojin kasar Sin don samun horo a fannin fasahohin sana’a, ta yadda za su zama kwararru a fannonin hada motoci da na’urorin sanyaya daki na AC, da kasar Najeriya ke bukata.
Sai dai, wadanne halaye na musamman ne na hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin aikin ilimi za mu iya gani, ta misalan da muka ambata?
Da farko, ana mai da hankali kan bukatun kasashen Afirka.
A kasashen Afirka, ciki har da Najeriya, ana bukatar samar da damammaki na karatu da aiki ga dimbin matasa. Saboda haka, ban da neman samar da damar karatu ga karin matasa, hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin aikin ilimi na kokarin hada bangarorin aikin ilimi da samun guraben aikin yi. Misali, jami’ar sufuri ta tarayyar Najeriya, da shirin hadin gwiwa na “Hanyar Siliki” da muka ambata, an tsara abubuwan da za a karanta ne, bisa tushen guraben aikin yi da ke akwai a kasar Najeriya.
Sa’an nan wata bukata ta daban ta kasashen Afirka ita ce raya masana’antu, da zamanantar da aikin gona. A wannan fanni, bisa nazarin da Tian Xiaohong, Malama ta jami’ar koyar da ilimin aikin malanta ta lardin Zhejiang na kasar Sin ta yi, an ce ta wasu shirye-shiryen da kasar Sin ta gabatar, da suka hada da “shirin hadin gwiwar jami’o’in Sin da Afirka”, da “shirin hadin kan Sin da Afirka a fannin koyar da ilimin sana’o’i”, an samar da dimbin kwararru masu ilimin aikin gona, da na noman itatuwa, da na injiniya mai alaka da ruwa, da dai sauransu, wadanda kasashen Afirka ke tsananin bukata don raya bangarorin masana’antu da aikin gona.
Ban da haka, ta misalan da muka gabatar, za mu iya ganin wani yanayi na daban na hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin aikin ilimi, wato ana dogaro kan bukatun da ake samu a bangaren masana’antu, a hadin gwiwar Sin da Afirka.
Kamfanonin kasar Sin suna zuba jari a nahiyar Afirka, da gina layin dogo, da gandun masana’antu, da ma’aikatu, inda suke bukatar samun dimbin kwararrun ma’aikata. Saboda haka suna son zuba jari don raya aikin ilimi a kasashen Afirka, ta yadda za su iya samun ma’aikata masu fasahohi.
Misali, Shagon Luban (Luban Workshop) wani wuri ne na musamman, da kasar Sin ta kafa a kasashe daban daban dake nahiyar Afirka, inda ake koyawa matasan Afirka fasahohin sarrafa injuna daban daban, ta yadda za su iya zama kwararrun ma’aikata cikin sauri, don biyan bukatun kamfanoni.
A nan za mu iya takaita halayyar musamman na hadin kan Sin da Afirka a fannin aikin ilimi zuwa lura da bukatun dukkan bangarorin kasashen Afirka da kasar Sin. Sa’an nan tushen wannan halayyar musamman shi ne manufar kasar Sin ta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ta Sin da Afirka. A bisa wannan manufa ake kallon ci gaban harkokin sauran kasashe a matsayin damammakin ciyar da kai gaba, da kokarin karfafa hadin gwiwa don neman samun walwala da ci gaba na bai daya. Ta hanyar nazari kan wannan manufa za mu iya fahimtar dalilin da ya sa kasar Sin ta zama babbar kasa da ta fi samun karbuwa a nahiyar Afirka, bisa sakamakon wani binciken ra’ayin jama’a da aka gudanar, wato idan wani abokinka ya kan yi hulda da kai cikin daidaito, sa’an nan yayin da kuke hadin gwiwa, zai iya lura da bukatun dukkan bangarori, da kokarin tabbatar da moriyar juna, to, wa zai ki hadin gwiwa da shi? (Bello Wang)