Abokai, yau ma “duniya a zanen MINA” ya zana wani hoto game da yadda al’umma ke rayuwa mai dadi a yankin Xinjiang karkashin tsarin hadin gwiwar yankin gabashin kasar Sin da na yammacinta.
Matar dake cikin wannan zane ta samu aikin yi ne a wani kamfani na yankin gabashin kasar, wanda ya dauki nauyin taimakawa wajen raya yankin Xinjiang, aikin da ya sa ta samu kudin shiga har ma ta sayi mota.
Mata irinta da dama na cewa, a baya ba su taba tunanin za su yi rayuwa mai nishadi kamar haka.
‘Yancin rayuwa da na samun ci gaba su ne hakkin dan Adam mai tushe, a kasar Sin, yankin gabas wanda ya fi samun bunkasuwa yana taimakawa yankin yamma dake dan koma baya, mataki ne na tabbatar da hakkin dan Adam mai tushe.
Wasu kafofin yada labarai na yamma sun shafawa kasar Sin bakin fenti cewa, akwai aikin tilas da keta hakkin dan Adam a yankin Xinjiang , wannan karya ce! (Mai zane: Amina Xu)