Hadin Kai Da Fahimtar Juna Tsakanin Sojoji Da ‘Yan jarida

A cikin kokarin da ake yi na kare kasa ta bangaren sojoji sukan samu matsala da mutane lokaci zuwa lokaci, kai har ma da ‘yan jarida wadanda su suna yin aiki ne saboda su sanar da al’umma abubuwan da suke faruwa akan al’amarin daya shafi sojoji.
A dalilin haka ne da kuma bukatar da ake da ita ta a kawo gyara dangane da hakan ne ma’ikatar tsaro ta shirya wani taron kasa na kwana biyu, wanda yake da taken”Hulda tsakanin fararhula da kiuma ‘yan jarida” wanda aka yi shi a jihar Kaduna.
Shi dai wannan taron an shirya shi ne saboda a kara bunkasa fahimtar juna tsakanin rundunonin tsaro da kuma ‘yan jarida, saboda sune wadanda ake fadi da kuma tashi tare da su, musamman idan ana bukatar yadda ya dace a tafiyar da labarun kare kasa. Wannan taron ya samar da wata dama ce ga wadanda suke da ruwa da kuma akan shi al’amarin, su kara duba yadda zamantakewar tasu take tare da kuma hulda, musamman ma su aikin nasu na yadda sukeduba labaran da kuma auna su saboda su yi ma kowa adalci. Musamman ma yadda ake cikin yadda al’amarin tsaro ya zamo kaka – nika yi, ga kuma harkar damukuradiyya.
A nashi jawabin Ministan tsaro Mansir Dan Ali ya yi kira da asamu fahimtar juna tsakanin ‘yann jarida da kuma jami’an tsaro, saboda a kara bunkasa tsaron cikin gida, da kuma dukkan al’umma da kuma dukiyoyinsu. Ya kuma ci gaban da bayanin cewar yana fatar za’a samu cimma babban dalilin da yasa aka dauki niyyar yin taron na kwana biyu, wanda daga karshen taron ne ake sa ran hakan. Saboda ai dama shi taken taron inda ya sa kan shi ne.
Ali ya ci gaba da bayanin cewar yanzu dukkan fafutukar da su sojoji suke yi ba wai dole ne ko wanne lokaci sai an samu cin nasara bane, amma kuma idan aka samu shi zaman lafiya tashin hankalin da ake yi aka amu saukin hakan, ai wannan shine abin so.
Soja shi ba wai mai son kasancewa ne cikin fada bane kamar yadda wasu suke yi mai kallon hakan, shi maison zaman lafiya ne, dansanda, ma’aikacin jakadanci, ma’aikatan samar da zaman lafiya, duk suna aikin ne saboda kara inganta hulda tsakanin su sojoji da kuma al’umma baki daya.
Ya kara jaddada bayanin cewar su kuma bangaren ‘yan jarida suma ba kamar yadda wasu ke kallon al’amarin aikin bane, sai sun tace da kuma yin adalci ga dukkannin al’umma wadanda suka kunshi gwamnati da kuma sojoji da kuma sauran rundunonin tsaro.
Mansur ya ci gaba da bayanin cewar rashin sanin yadda sojoji suke tafiya da yyukan su, da kuma su yadda ‘yan jaridar suke aiwatar da nasun, amma daga karshe dai babban abin bukata anan shine su samu hadin kai tsakanin su saboda a samu kare kasa.
“Shi babban abin fahimta anan shine ita matsalar da sojojin su kan shiga ana samun tane, lokacin da ake cikin yaki ko kuma al’amari can daban lokacin ne aka fisamun matsala tsakanin sojoji da kuma ‘yan jarida.
Ministan ya kara jaddada cewar suma sojoji ya kamata su san cewar ban komai bane sa suyi kane- kane su hana asan halin da ake ciki, dole ne su bada dama a san hakikanin gaskiyar al’amarin da ake ciki wanda ya shafi su sojoji, da kuma kare su jami’an watsala labarai ko kuma ‘yan rida. Suma ‘yan jarida akwai bukatar su bi dokokin da suka shimfida aikin nasu, duk kuma bin da za su bada labari dangane da shi, su tabbatar da gaskiyar, su kuma yi ma dukkan bangarorin adalci.
Ya kuma kara yin kira ga bangaren yada labaran ko kuma su ‘yan jaridar su yi hanakali ko kuma su bi a hankali akan abin da shi labarin ya kunsa, musamman ma idan anab fagen fama ne, na kada su rika bayar da labaran farfaganda wadanda kuma su abokan gaba sune ake nuna cewar suna samun galaba, su kuma wadanda suke da nasarar a rika fadin karya da karairayi dangane da su. Irin wadannan labaran sune suke ba abokan gaba kwarin gwiwa. Ya yi kira da su mahalarta taron da cewar su samar da wasu hanyoyi wadanda za su taimaka, saboda a samu kyakyawar alaka wadda za’a kawo karshen ita maganar kiki- kaka atsakanin su. Saboda idan ka samu ita damar za’a kara samun ci gaba wajen yaki da ake yi da aikata laifi da kuma su wadanda suke samar da yanayin na aikata laifi. Daga karshen shi taron mahalarta shi taron sun yi kira da cewar a samu damar horarwa tsakanin su ‘yan jarida da kuma su sojoji saboda a kara samun wata dama ta ta fahimtar junan su, saboda daga karshe ana iya lura da cewar duk bori daya bane suke yi ma tsafi, bama kamar idan aka yi la’akari halin da ake ci na yaki da Boko Haram da kuma sauran ‘yan tada kayar baya.
Bugu da kari kuma su mahalarta taron su kara yin kira da cewar a rika kiran shi taron na hadin kai da kuma fahimtar juna akai-akai saboda, a samu yadda za ‘a sake ma ita tufkar hanci tsakanin su sojoji da kuma ‘yan jarida.
Ita dai wannan shawarar tana daga cikin wasu abubuwa goma sha 11 wadanda suka kasance cikin shawarwarin da suka bada bayan shi taron, wanda Malaman jami’oi da kuma, manyan jami’an sojoji, manyan masu gidajen watsa labarai, Editoci, sai kuma wasu jami’ai na sauran rundunonin tsaro da kuma kwamitin tsaro na sirri.
Sauran abubuwan da jawabin bayan taron ya kunsa sun hada da ya kamata su banagaren watsa labarai da cewar su rika duba yadda al’amarin tsaro yake na kasa, kafin su kai ga sakin wasu labarai ko kuma buga su, wannan kuwa bai kamata ayi la’akari da yadda shi labarin ya ke ko kuma abin da ka iya faruwa bayan an bayyana shi.

“Inda aka san in an bayyana wani labari zai iya shafar ko kuma kasancewa matsala wadda zata iya shafar tsaron kasa, to wannan labarai bai ma kamata abuga shi, ko kuma sanar da shi ta ko wacce hanya.
Shi al’amarin tsaro bai kamata ace ya ta’allaka bane hannun sojoji kawai, wannan ba haka bane, saboda kuwa shi al’amari ne wanda ya shafi kowa da kowa.
Kamar dai yadda ita sanarwar bayan taron ta bayyana su masu ruwa da tsaki akan al’amarin sun yi kira da ita ma’aikatar, da hadin gwiwa da mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro su fidda wani tsari ko kuma wata manufa, ta yadda za’a tafiyar da labarin daya shafi tsaro.
Wakilin mu ya bada rahoton cewar taron wanda aka shirya shi saboda a samu wani hadin kai da kuma fahimtar juna, tsakanin su jami’an tsaro da kuma ‘yan jarida, su kasance su abokan tafiya ne, muddin dai ana maganar al’amarin daya shafi tsaron gida. Wannan wata hanya ce wadda ta samar da dama yadda za su sake duba yadda suke tafiyar da hulda tare, da kuma inganta ta kamar yadda ya dace.
Shima a tashi mukalar daya gabatar tsohon mai ba tsohon Shugaban kasa Olusegun Obaasnjo shawara akan harkokin tsaro Olusegun Adeniyi, kira ya yi da rundunar sojoji cewar, su tabbatar da sun bada dama ajen aiki da shawarwarin da aka bayar, saboda a samu dama yadda za’ayi aiki kafada da kafada domin cimma burin a inganta ci gaban kasa.
Bugu da kari shi dai Adeniyi shine Shugaban kwamitin Editoci na jaridar This Day kara bayyana cewar shi aikin sojoji na kare kasa yana tattare da nashi matsalolin, wadanda kuma akwai bukatar da a bayar da taimako, wadanda suke bukata, wannan taimakon kuma ana iya samun shi daga wurin wadanda suke da ruwa da tsaki suma, wato bangaren watsa labarai ko kuma ‘yan jarida. Ya kuma kara cewar su ma bangaren watsa labarai suna da tasu gudunmawar da za su bayar wadda bata uce kda su maida aikin su sojoji ya kasance wanda yake da wahala fiye da cikin halin da suke ciki yanzu. Amma duk da hakan su ma sojoji ya yi kira gare su da cewar suma kada su dauki doka a hannun shi, idan alal, misali an buga wani abin da bai yi masu dadi ba.
Ya kara yin bayanin cewar su “Sojoji koda wanne lokaci abin da suke bukata duk wasu labaran da suka shafe su, gani suke yi kamar ba’a fadar gaskiya, su kawai so suke yi a rika fadin nasarar da suka samu kawai bama kamar a fagen daga,idan kuma son samu ne wato idan abin har zai yiyu kada a bayyana wani rashin da suka samu, ko kuma wata masifa wadda ta aukar masu”
Bugu da kari kamar dai yadda ya kara haskakawa cikin nashi tunanin “Hakanan ma su sojoji basu bukatar wasu bayanai na bangaren watsa labarai ko kuma ‘yan jarida akan taka hakki ko kuma cin mutuncin dan Adam da aka yi, musamman ma idan abin ya fito ne daga Amnesty International. Ya yin duk shi wancan al’amari ne ya fi tayar masu da hankali, har yanzu abin da suka kasa fahimta shine ba za su taba samun nasarar yaki ba, bama kamar wanda suke yi na al’amarin daya shafi tayar da haddasa fitina ba tare da sun samu taimako daga bangaren watsa labarai ba.
Da ya ci gaba da karin bayanai na kawo karshen shi taron da kuma nannade ita Tabarmar ya ce idan ana bukatar samun nasara”Amma wannan har sai idan sun yarda kuma amincewa ba za su taba samun nasara ba suna masu gardama inda suke ganin saboda suna da wata dama wadda Allah ya basu, duk da yake dai da akwai wasu shawarwarin da aka bayar, amma babbar manufa ita ce su wadanda alhakin dukkan al’amuran suka rataya a gare su, na tabbatar da duk an aiwatar da su,saboda a samun dankon zuminci da kuma son juna tsakanin su sojoji da kuma ‘yan jarida, saboda su kara amafani ga junan su da kuma sauran al’umma.

Exit mobile version