Abokai, ko kun san tsawon layukan dogo da hanyoyin mota da kamfanonin Sin suka taimaka wajen ginawa a Afrika?
Tsawon layukan dogo ya kai kilomita dubu 10, a yayin da na hanyoyin mota ya kai kusan dubu 100. Ban da haka kuma, kamfanonin sun gina gadoji fiye da dubu da tashoshin jiragen ruwa kimanin dari, da kuma dimbin makarantu da asibitoci, kamfanonin sun kammala wadannan ayyuka kan lokaci tare da tabbatar da ingancinsu.
Yau cikin “duniya a zanen MINA”, na zana wani hoto kan yadda wani kamfanin Sin ya gina layin dogon dake tsakanin biranen Abuja da Kaduna dake kasar Najeriya, wanda na taba samun damar halartar bikin kaddamar da shi a Abuja.
Wani fasinja mai suna Babatunde Lawal, wanda ya kan yi tafiye-tafiye tsakanin wadannan birane biyu ya ce, “wannan layin dogo ya rage lokacin da za a kashe ta zirga-zirga a tsakaninsu, kuma jirgin na da inganci matuka.
Kazalika ya samar da guraben aikin yi da dama, har ma kasuwar dake gefen tashar na kara wadata. Ba mahadar wadannan birane biyu kadai layin dogon ya zama ba, har ma da zama shaidar dankon zumuncin kasashen Najeriya da Sin.”
Kungiyar masana ta kasar Kenya ta IREN ta ba da rahoto a kwanan baya cewa, nazarin jin ra’ayin jama’a na nuna cewa, ayyukan da Sin take yi sun fi na EU inganci.
Ba shakka, manyan ababen more rayuwa da kamfanonin Sin suka gina a kasashen Afrika na da inganci matuka, kuma suna samun karbuwa daga mazaunan wuraren, matakin da ya taimakawa kasashen Afrika wajen samun bunkasuwa da dogaro da kansu.
Yaya ingancin wadannan ayyuka, kuma wane ne ke kokarin taimakawa al’ummar Afirka, to jama’ar Afirka ne za su ba da amsa, kuma ba wanda zai iya shafawa irin wannan hadin gwiwa da dangantaka dake tsakaninsu bakin fenti ko kadan. (Mai zane: MINA)