Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai kawo muku yadda ake hada Kek.
Abubuwan da za ku tanada:
Fulawa, Suga, Madara, Kwai Bekin Fauda, Bota, Koko Fauda. Sai abubuwan zubawa abin yin Kek kenan:
Yadda za ku hada:
A tankade fulawa da bekin fauda da madara a aje gefe, a zuba bota a roba a juya ta fara fari ta narke ko kuma za ki iya dan dora ta a wuta ta narke, amma kar ta yi zafi sosai, sai ki zuba suga ai ta juyawa har sai sun yi fari sannan a fasa kwai daya bayan daya ana yi ana juyawa sosai yadda zai hade jikinsa.
In an gama a kawo wannan fulawar da aka tankade su sai a rinka zubawa ana juyawa har a gama zubawa sai a sa fulawa ba’a juyawa sosai in an zuba fulawar sai ki dauko mazubi ki raba kwabin biyu sai dayan ki tankada koko fauda a kai ki sa kalar kofi ki juya
Ki kawo gwangwanayenki ki shafa musu bota ko kisa tankaden nan ki duba fari a gefe me koko ma a gefe shike nan sai a gasa.