Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
Yau kuma za mu yi magana akan yadda ake hadin Lemon Kayan Marmari da Yoagot.
Abubuwan da uwargida za ta tanada:
Suturoberi, Kiwi, Mangwaro, Lemon zaki, Fasa Dabur, Yagot, filawa.
Yadda uwargida za ta hada:
Da farko za ki dakko kowanne daga cikin kayan marmarin sai ki gyara su kowanne ki zuba a abu daban kar ki hada su wuri guda, sannan sai ki dauke su daya bayan daya nika su duk wanda kika nika za ki tace shi sai ki zuba kowanne daban ba hada su za ki yi ba, sai ki dakko kowanne ki zuba musu filawa ki kwaba ya yi tauri kamar yadda ake kwabin cincin za ki ga kowanne ya ba da kalar kayan marmarin da kika hada shi, sai ki dakko kowanne ki dora shi a kan cafin bot, sannan ki tattada su kamar yadda za ki tada cincin sai ki yayyaka su a tsaye da kuma a kwance za ki ga ya zama kanana-kanana. Sannan sai ki dauki kowanne guda daya ki mulmula shi bayan kin mulmula su za ki iya hada su waje guda sai ki dora ruwa a wuta ya tafasa, sannan sai ki zuba su cikin tafasasshen ruwan sai ki barsu su kara tafasa tare, sannan sai ki kwashe su a cikin ruwan zafin ki zuba a jug ko kofin idan yanzu za ki sha sai ki dakko yagot ki zuba a kai, idan kina so za ki iya zuba dan suga kadan haka amma ba dole bane. Asha dadi lafiya.