Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa daku a cikin wannan shiri namu mai farin jini da albarka na ado da kwalliya.
Yadda Uwargida za ta gyara jikinta ta fito tana gyalli:
Àbubuwan da ake bukata:
Sabulun salo, Sabulun wanka, majigi, man kwakwa kadan, man zaitun shima kadan
Lemon tsami kidan yanki kada shima amma idan kinsan baya saki koraje a fuska saboda wasu idan suka yi anfani da lemon tsami yana sasu koraje a fuska, jar kanwa kadan itama, alobera kamar guda uku, kwanduwar kwai kamar uku itama
Yadda ake hada su:
Zaki dauki Sabulun salo kisashi acikin turmi sannan ki dauko Sabulun wanka shima kisashi a cikin turmi ki hadasu kita dakawa harsai sun daku wato sun hade jikinsu sun zama abu daya shi ne sun dako, sannan ki kawo dukka abubuwan da muka ambata ki zuba su a cikin turmin amma kidan rage man kwakwa wanda idan kin zo curawa zaki dangwala hannunki a ciki ki hadesu gaba daya ki yi ta dakawa har sai sun hade, daganan sai ki fara cura shi yadda zaki cura zaki gutsira sabulun salon a hannunki sai ki dan lakuta man kwakwar a hannunki kinsan dama mun ce zaki rage man kwakwa saboda curawa to wannan wanda kika rage shi zaki yi amfani da shi saboda kar sabulun ya kamamiki hannu kina curawa haka ki molmole shi to wannan Sabulun shi ne sabulun wankanki kafin kishiga wanka zaki dan iya shafa shi a fuskarki kamar na minti biyar haka zakiga yadda fatar jikinki zai yi kyau cikin sati biyu da yarda Allah.