Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu na girki adon mata.
Hadin wannan Sandwich:
Abubuwan da yakama uwargida ta tanada:
Biredi, Nama, kabej, Karas, Bama, kecuf, Magi da gishiri, Tattasai, Albada, mai
Yadda uwargida za ki hada:
Da farko za ki tafasa naman ki sannan ki soya shi sai ki ajiye shi a gefe, sai ki jajjaga tattasan ko tarihu duk wanda kike so ki yanka albasa sannan ki zuba mai kadan haka a abin suya sai ki dorashi a wuta sannan ki zuba albasa sai ki zuba tattasan da kika jajjaga sai ki dan soya sama sama sannan ki zuba dan magi da gishiri da kuri ki juya su sannan ki dakko wannan naman da kika soya sai ki zuba a ciki ki dan jujjuya su, su hade jikin su sannan ki sauke.
Sai ki dakko kabej ki yayyanka ki wanke shi ki zuba a kwando saboda ya tsame ruwa, sai ki wanke karas din ki gurza shi ba yankashi zakiyi ba gurzashi za kiyi ki ajiye a gefe, sannan sai ki samu wani bowl haka ki zuba bama dai dai yadda zata isheki sannan ki zuba kecuf din a cikin bamar sai ki zuba madara amma ki damata da dan ruwa sai ki kawo yaji kadan haka ki zuba sai ki damesu gaba daya su damu, sannan sai ki hada kabej da karas din waje daya ki dakko wannan bama da kecuf din da kika dama sai ki raba shi gida biyu saboda zaki ajiye wanda za ki shafawa biredin, sauran kuma sai ki zuba a cikin kabej da karas din ki gaurayasu gaba daya sannan ki dakko biredin ki mai yanka yanka sai ki shafa masa wannan sauran hadin bamar da kika rage sannan ki debo hadin kabej din da kika hada sai ki zuba a saman biredin sannan ki dakko soyayyan naman ki zuba a kai sai ki dakko wani biredin ki rufe haka zakiyi harki gama shikenan kin gama hadashi. Aci dadi lafiya