Hajiya Hadiza Bala Usman ta jaddada cewa, ta yi aiki a Hukumar Tashoshin JIiragen Ruwan Nijeriya (NPA) ne ba tare da wata matsala ba kuma za ta yaki duk wani da yake kokarin bata mata suna da kyakyawar tarihin aikinta.
“A makwannin da suka gabata ne, wata abokiyata ta jawo hankali na a kan shirin da wasu suke yi na bata mani suna ta hanyar yada karya a kaina a kafafen yada labarai, gangami ne dake fitowa daga wadanda suke tunanin na zama musu kariya a hankoronsu na cimma wani burinsu a rayuwa.
“Ban dauki lamarin da wani muhimmanci ba har sai da na ga wani rahoto da aka kai hari gare ni da ayyukan dana yi a yayin da nake shugabantar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa, NPA. Duk da naga rahoton na yi watsi da shi musamman ganin wanda ya rubuta ba shi da kwarin gwiwa sanya sunanna kai tsaye a gwiwar saboda rashin gaskiya.
“Amma a ranar Alhamis 15 ga watan Yuni 2023 sai ga wani rahoton a wasu jaridun Arewacin kasar nan ciki harda jaridar Blueprint a bangarensu na yanar gizo inda aka bayyana suna na kaitsaye. A daidai wannan lokacin ne na yanke shawarar mayar da martanin da ya dace.
“Kanun labarin da aka sanya a wasu jaridun ya kasance kamar haka: “Kada ka nada tsofeffin ma’aikatan gwamnati da ake zargi da sace kudin gwamnati—Wata kungiya ta gargadi Tinubu” yayin da kanun na jaridar Blueprints ya kasance kamar haka: “Kada ka nada tsofeffin ma’aikata masu kashi a gindi, wata kungiya ta shawarci Tinubu.”
“Rahoton ya fito ne daga takardar sanawar wata kungiya mai suna ‘Leadership Legacy Int’l (Centre LLI)’ inda suka ba da misali da ni Hadiza Bala Usman, a matsayin tsohuwar ma’akaciyar da ake zargi da almundahana a yayin da nake shugabantar NPA.
Jaridar Blueprint, ta cigaba da bayyana cewa, wai na yanke hulda da dangantakar NPA da kamfanin Intels” wai duk da abubuwan da kamfanin ta yi wa NPA.
Sun kuma zarge ni da rashin sasanta rikicin tsakanin ‘Ladol’ da daya daga cikin abokan huldar su, Messrs Samsung Ltd…”. Sun kuma kara da cewa, “Akwai rahottanin da ke nuna cewa, ana shirin tursasa wa shugaban kasa ya nada wasu mutane da suke da kashi a gindi a gwamnatinsa.
Bukatar shugaban kasa ya nada mutane masu sahihan tarihi yana da matuka muhimmanci a wannan lokaci fiye da dukkan lokaci,” in ji rahoton.
In aka lura da rahoton za a lura tamkar ana nuna cewa, ina cikin mutane da suke da kashi a gindi kuma yakamata shugaban Tinubu kasa ya yi hattara dasu.
Bari in fara da tunatar da kungiyar da ta ruwaito rahoton don kuwa ta rasa kangado, da shirmanmun da ke daukar nauyinsu cewa, Allah madaukakin Sarki ne yake da ikon bayar da Mulki kowanne iri ga wanda yaso. Saboda haka kada su yi tunanin samun wani mukami ta hanyar bata wani da bai yi musu laifi ba.
Koma bayan zargin da suke yi, ba a cire ni a ofis saboda wani abin da ya shafi almundahana ba, ko kuma abin da ya yi kama da haka.
Duk da tuni labarin ya karrade kafafen sadarwa, amma duk mai neman sanin gaskiya bashi da mastalar sanin gaskiyar. Ina dai kokarin ilimatar da masharrantar ne da suka kasa bayyana fuskokinsu.
An yi kuskuren zargin hukumar gudanawar NPA a karkashin jagorancina da rashin mika naira biliyan 165 ta asusun gwamnatin tarayya mai suna ‘Consolidated Rebenue Fund (CRF)’, zargin da ya fito daga tsohon ministan sufuri Rt. Hon Chibuike Rotimi Amaechi.
Daga baya ya samu amincewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na in koma gefe saboda girman zargin da aka yi har sai kwamitin da ya kafa na gudanar da binciken ta gama aikinta.
Bayan aikin wata 8, kwamnitin da ministan ya nada bai iya tabbatar da laifin da ake zargi na ba, basu iya tabbatar da wani laifi tare da ni ba a kan rashin saka Naira Biliyan 165 billion a asusun gwamnatin tarayya, wanda shi ne dalilin da Ministan ya a nemi izinin shugaban kasa na in koma gefe har a kammala bincike.
Wadannan kuma basu a cikin takardar tuhuma mai taken, “Zargin aikata ba daidai ba sakamakon rahoton binciken harkokin Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa NPA daga 2016 zuwa 2021.”, wanda babban sakataren ma’aikatar sufuri, Dakta Magdalene Ajani ya bani bayan kammala binciken kwamitin da Ministan ya kafa a ranar 28 ga watan Janairu 2022.
Amma koma bayan abin da suka bayyana wa al’umma, rahoton ya nuna cewa, duk da kuma ministan ya ki bayyanawa al’umma cikakken rahoton – sun gano cewa, na zuba fiye da Naira Biliyan 182 cikin asusun gwamnatin tarayya na ‘Consolidated Rebenue Fund (CRF)’ a daidai lokacin da suka gudanar da binciken.
Masu gaskiya a cikin masu ruwa da tsaki a bangaren masa’ananta harkokin jiragen ruwa za su yi wa bayanan da ‘Centre LLI about Intels’ da ‘Ladol’ suka don ya nuna tsananin jahilcin su da rashin adalcinsu a kan lamarin.
Misali sun bayyana cewa, na yanke dangantakar NPA da ‘Intels’, amma kuma ainihin abin da ya faru shi ne karewar wa’adin daya daga cikin bangarori 8 na huldar da NPA ke da shi da ‘Intels’, wanda kuma shi ne abin da ya shafi ayyukan kananan kwalele, wannan yana kara nuna jahilcin wadanan mutane da kuma yadda suke shirya sharrin.
Kwangilar NPA da Intels ya fara ne tun shekarar 1997, kafin wa’adin ya kare a shekarar 2020, kafin nan NPA ta yi ta takaddama da su a kan rashin biyayya ga dokokin gwamnatin tarayya musamman dokar gwamnatin tarayya na cewa, dole a sa dukkan kudin shigar gwamnatin a asusun na da ake kira da ‘Treasury Single Account (TSA)’. A lokacin ina shugabancin NPA, INTELS ta rike fiye da Dala 264,932,666.91 na kudaden NPA wanda suka ki biya a asusun gwamnatin tarayya.
Rikicinmu da Intels ya shafi kamfani ne dake daukar kansa tamar ya fi karfin dokokin kasa da dokokin NPA, a karkashin shugabancina a NPA na yaki wannan na kuma daidata lamurran.
Haka kuma kamfanin ‘Ladol’ ya karya dokokin sharuddan yarjejeniyar da suka kulla da NPA, mun yi dukkan abin da muka yi daidai da yarjejeniyar da aka kulla dasu tun da farko. Niyyata a dukkan lamarin shi ne aiwatar da abin da dukkan bangarorin har da ita NPA za su yi aiki da yarjejeniyar ba tare da wata matsala ba.
Bayani dalla-dalla na abin da ya faru tun daga takardar tuhuma da ma’aikatar sufuri ta ba ni da yadda ta kaya a kwamitin binciken da aka kafa duk suna nan a cikin littafin da na rubuta mai suna, “Stepping on Toes: My Odyssey at the Nigerian Ports Authority”. Na rubuta littafin ne don tsage gaskiyar abin da ya faru da kuma katse hanzarin kungiyoyi wadanda suke yada karya kamar yadda suka yi a rahoton jaridun da suka buga.
Jariar Blueprint ta kuma ce, wai ana gabatar da ni a gaban shugaban kasa, wannan abin dariya ne matuka.
Bari in tunatar da wannan kungiyar da kuma gidajen jaridar da suka buga labarin cewa, na yi aiki na kut da kut tare da Shugaban Kasa Tinubu a matsayin mataimakiyar darakta mai kula da gudanarwa a kwamitin yakin neman zaben shugaban kkasa na jam’iyyar APC, saboda haka kasancewata a kusa da shi wani abu ne sakamakon aikin da muka yi tare da shi kuma babu wani da zai iya kawo wa wannan dangantakar cikas.
Daga karshe ina kira ga kungiyoyi da mutane irin su ‘Centre LLI’ (da masu daukar nauyinsu), da gidajen yada labarai da su guji buga labarai na kage a kai na kamar irin wannan da ake magana akai.
In har ba a bar irin wannan ba, bani da zabi illa in nemi hakki na kamar yadda dokar kasa ta ba ni dama a kan duk wani abin da aka buga akai na da ya nemi bata suna da aikin dana yi a NPA.