A yau Alhamis rahotanni daga Kasar Saudiyya na cewa wasu alhazai biyu Maza daga jihar Kano sun rasu, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na hukumar alhazan Nijeriya na jihar Kano Alhaji Nuhu Badamasi ya sanar ta wayar tarho daga Makkah.
Badamasi, yace, a yanzu haka an binne alhazan a Makkah, alhazan da suka rasu sun fito daga kananan hukumonin Dala da Doguwa dake Jihar Kano.
Badamasi, ya kara da cewa, a ranar 15 ga watan da muke ciki ne za a dawo da alhazan jihar Kano gida daga Saudiyya.