Daga: Umar Faruk, Birnin-kebbi
Maimartaba Sarkin Zuru Manjo Janar Mairitaya, Sani Sami Gomo na biyu, kuma amirul Hajji na jihar kebbi na bana, ya gabatar da jawabin bankwana da gargadi ga mahajjatan aikin hajji sawun farko 553 na jihar kebbi, da zasu gudanar da aikin Hajji na 2017 a kasar saudi Arebiya, domin su kasance jakadun jihar kebbi da kuma kasar Nijeriya don kauce wa ayyukan da zai iya jawo musu matsalar ga kansu a lokacin da suke ƙasar mai tsarki.
Sarkin na Zuru, ya yi gargadin ne a filin jirgin sama na kasa da kasa na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi yayin gabatar da jawabinsa na ban kwana ga mahajjata da suka tashi zuwa madina dake kasar Saudiyya a ranar assabar da misalin karfe 10:45 na dare a matsayin sa na amirul hajji na jihar kebbi na bana.
Har ila yau, ya hori mahajjata su kasance masu da’a da ladabi da biyaya ga dokokin kasar saudiya a lokacin da su ke kasar.
Bugu da kari basaraken ya shawarce su da cewa aikin hajji aiki ne wanda ake sadaukar da kai wurin yin sa. Domin aikin hajji yana daya daga cikin shikashikan musulunci guda biyar, saboda haka duk wanda Allah yaba iko to ya yi kokari ya gudanar da aikin yadda ya kamata.
Hakazalika ya roki mahajjata da su gudanar da addu’a ga jihar kebbi, kasar Nijeriya da kuma Shugaba Muhammadu Buhari da kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali da hadin kai ga mutanen kasar Nijeriya.
Mahajjata da suka tafi sawun farko daga jihar kebbi sun fito ne daga kananan hukumomin Fakai, Danko-Wasagu, Bunza, Yauri ta Arewa inda suka tashi a filin jirgin sama na Ahmadu Bello da ke Birnin-kebbi malakar Gwamnatin jihar ta kebbi zuwa Madina kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana. Wadanda kanfanin jiragen Mad Airline ya dauka.
Daga sarkin Zuru Sani Sami, ya yi wa mahajjatan fatar alhairi da kuma yin aikin hajji madabuliya a kuma je lafiya a dawo lafiya.