Sakataren zartarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai na Jihar Nasarawa, Malam Idris Ahmad Almakura, ya ce Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) ta cancanci yabo da jinjina ba yin Allah wadai ba wajen tafiyar da ayyukan hajjin bana.
Shugaban hukumar alhazai, Alhaji Zilkrullah Kunle Hassan, ya fuskanci suka sosai biyo bayan wahalhalun da alhazan Nijeriya suka sha a masha’ier musamman a Mina inda aka tilastawa wasu mahajjata kwana a waje saboda rashin tantuna. da sararin kwanciya.
- Duk Maniyyatan Da Muka Yi Wa Biza Sai Sun Sauke Farali Da Yardar Allah – NAHCON
- Hajjin Bana: NAHCON Ta Samar Da Biza 73,310, Tare Da Kai Alhazai 46,000 Kasar Saudiyya
Samar da tantuna da ciyar da alhazai a Masha’ier ba hakkin hukumar NAHCON ba ce, kamfanin kasar Saudiyya, Mutawwif, wanda ya rataya a wuyansa na samar da isassun tantuna da ciyar da mahajjatan Nijeriya sama da 95,000 ne ya gaza cimma abin da ake bukata.
Sai dai Almakura a zantawarsa da LEADERSHIP a Makkah ya yi amanna duk da karancin tantuna da karancin abinci ga ‘Yan Nijeriya a Mina bai isa dalilin yin watsi da kokarin NAHCON ba, yana mai cewa, a mafi yawan lokuta, shugabancin hukumar na yin abin da ya dace, kuma sun cancanci yabo maimakon zargi.
“Ina son in yaba wa shugaban Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Alhaji Zilkrullah Kunle Hassan, da tawagarsa da shugabannin hukumar” Cewarsa.