Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano ta bada sanarwar canja kamfanin jirgin sama na Azman Air zuwa Max Air a matsayin kamfanin da zai yi jigilar maniyatan Jihar zuwa Saudiyya domin gudanar da Hajjin 2022.
NAHCON ta sahalewa Azman Air yin jigilar maniyyatan Kano bayan da kamfanin ya gaza cimma matsaya da hukumar.
- Abubuwa 5 Da Zaku So Sani Game Da Biodun Sabon Gwamnan Ekiti Mai Jiran Gado
- Ya Fada Rijiya Yayin Da Yake Kokarin Jefa Mai Masa Aiki Don Yin Tsafi Da Shi
Sai dai kuma Shugaban Hukumar Alhzai na Jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Dambatta, ya musanta cewa hukumar ta ki amincewa da kamfanin Azman, inda ya tabbatar da cewa basu taba kulla alakar aiki a junansu ba.
Sai dai kuma ya ce hukumar na tattaunawa da NAHCON kan kamfanin da zai yi jigilar maniyyatan na Kano.
A wani taron manema labarai da ya yi a ranar Lahadi, Dambatta, ya ce sun kammala tattauanawa da NAHCON, inda suka tsayar da matsayar kamfanin jirgin sama na Max Air shi ne zai yi jigilar maniyyatan Jihar Kano zuwa kasa mai tsarki.
Ya ce dama rashin kammala tattauanawa da hukumar NAHCON ne ya hana hukumar jin dadin alhazai ta Kano ta sanar da kamfanin da zai yi jigilar maniyatan jihar.
Babban sakataren ya kuma ce zasu fara tantance lafiya maniyyatan a ranar Litinin, domin tabbatar da cewa ba a samu maniyyata masu dauke da cutar kyandar biri ko kuma cutar Korona ba.
Ya bada tabbacin kowanne lokaci daga yanzu za a fara jigilar maniyyatan Kano zuwa kasa mai tsarki.