Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), ta bayyana cewa Nijeriya ta yi rashin alhazai 14 a Saudiyya daga fara gudanar da aikin hajjin 2023 zuwa yanzu.
Shugaban tawagar likitoci ta NAHCON, Usman Galadima ne ya bayyana haka a wani taro, bayan Arafat da masu ruwa da tsaki a jiya Lahadi a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
- Hajjin 2023: Gobe Talata Za A Fara Jigilar Alhazan Nijeriya Zuwa Gida
- Dikko Radda Ya Ba Alhazan Katsina Su 4,634 Kyautar Miliyan ₦278 A Kasar Saudiyya
Galadima ya bayyana cewa mahajjata bakwai sun rasu kafin Arafat, inda wasu guda shida kuma su ka rasu a cikin kwanaki biyar na Mashair (babban lokacin Hajji da ake yin zaman Mina) sannan karin mutum daya ya rasu bayan Arafat.
Ya ce da yawan mahajjatan sun rasu sakamakon turmutsutsu, yayin da wasu suka rasu sakamakon rashin lafiya.
“Mun samu rahoton mutuwar mutane shida a Mashair, hudu sun mutu a Arafat, sauran biyun kuma sun mutu a Mina.
“Tun da fari, mun rasa mahajjata bakwai kafin Arafat kuma a yanzu haka an sanar da ni cewa mun rasa wani alhaji. Wannan ya kawo adadin wadanda suka rasu zuwa 14.
“Yawan mace-mace ya yi kama da na 2019,” in ji shi.
A ranar Talata ne da ta gabata Alhazai daga sassan duniya daban-daban suka hau arfa, yayin da kuma sauran Musulmi suka gudanar da Idin babbar sallah a ranar Laraba.