Adadin mahajjatan Nijeriya da suka isa kasar Saudiyya ya kai 24,324 ya zuwa yanzun yayin da Alhazan Jihohin Sokoto da Zamfara suka isa birnin Madina lafiya don gudanar da aikin hajjin bana su 752.
Alhajazan na jihohi biyun, sun hada da maza 491 da mata 261, kamfanonin jiragen sama na Saudiyya, Flynas FlightXY5624 da Flynas FlightXY5712 suka yi jigilarsu daga filin jirgin saman Sultan Abubakar III, Sokoto da karfe 10:34hrs da karfe 14:58 kai tsaye zuwa filin jirgin saman Yarima Mohammad bin Abdulaziz, Madina.
A ranar 25 ga watan Mayu ne dai aka fara jigilar maniyyata daga Nijeriya zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin 2023 a lokacin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda tsohon karamin ministan harkokin waje, Zubairu Dada ya wakilta, inda jirgin farko a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe Abuja ya tashi da maniyyata 472 na jihar Nasarawa da jami’an hukumar Alhazai (NAHCON) su 27.
A wani sabon kididdiga da hukumar NAHCON ta fitar, ya nuna cewa, adadin maniyyatan Nijeriya maza a Saudiyya a halin yanzu ya kai 14,491 sai mata 9,692.