Hukumar kula da jin dadin alhazai ta Jihar Bauchi ta ce, ya zama dole kowani maniyyancin da zai sauke farali a hajjin bana sai an masa riga-kafin foliyo.
Babban sakataren hukumar, Imam Abdulrahman Idris, shi ne ya sanar da hakan yayin da ke ganawa da manema labarai a shalkwatar hukumar da ke Bauchi.
- Bukatar Kawo Karshen Karin Kudin Kiran Waya Da Na Data
- Gwamnati Ta Jaddada ƙudirin Kare ‘Yancin Faɗin Albarkacin Baki Da ‘Yancin ‘Yan Jarida
Ya ce, adadin maniyyata 2,200 ne suka yi rajista da biyan kudin kujera ta hannun hukumar domin neman sauke farali a yayin aikin hajjin 2025 a kasa mai tsarki ta Saudiyya Arabiyya, kuma dole ne dukkanninsu sai sun amshi takardar gwajin riga-kafin foliyo makwanni shida kafin tafiya zuwa Saudiyya.
Ya yi gargadin cewa dukkanin maniyyancin da ya ki amsar riga-kafin, to ba zai samu damar tafiya zuwa Saudiyya ba, “Wannan umarnin ya zo ne daga hukumar kula da jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON) a wani yunkuri na daukan matakan tabbatar da kula da lafiya da kare maniyyatan Nijeriya.”
Babban sakataren ya kuma sanar da cewa hukumar ta rufe amsar kudaden tafiya aikin hajjin bana tun daga ranar 17 ga watan Maris. Ya kuma ce nan da mako biyu dukkanin takardun tafiya, jakunan sanya kaya, rigunar da sauran ababen da suka dace duk za a kawo su.
Ya nemi wadanda har zuwa yanzu ba su dawo da fom dinsu ba da hoto da su gaggauta yin hakan domin su samu biza daga kasar Saudiyya Arabiyya.
Shugaban ya nemi maniyyatan da su bai wa hukumar cikakken hadin kai domin samun nasarar gudanar da aikin hajjin cikin nasara da kwanciyar hankali.
Bayanai sun yi nuni da cewa wadanda suka fara ajiye kudin kujeru amma ba su kammala biya ba su na da zabin ko su amshi kudadensu ko su bari a asusun hukumar har zuwa aikin hajjin badi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp