Gwamna Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle ya nada kakakin majalisar dokokin jihar, Alhaji Nasiru Magarya, a matsayin jagoran Alhazai na jihar don gudanar da aikin hajjin wannan shekarar ta 2022.
An bayyana hakan ne acikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Kabiru Balarabe ya sanya wa hannu a Gusau ranar Litinin.
“Muna sanar da jama’a cewa Gwamna Bello Matawalle ya amince da nadin Alhaji Nasiru Magarya, kakakin majalisar dokokin Jihar Zamfara a matsayin jagoran mahajjata kuma shugaban tawagar gwamnatin jihar a hajjin bana.
“Ya kuma amince da nada babban sakatare a ma’aikatar ayyuka da sufuri, Garba Ahmad, a matsayin sakataren tawagar domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2022.
“Gwamnan ya kuma amince da nadin da akayi na wasu mambobin tawagar kamar haka:
“Shugaban majalisar dokokin jihar, Alhaji Farouk Musa Dosara; kwamishinan harkokin kananan hukumomi, Abubakar S-Pawa; Sarkin Talata-Mafara, Alhaji Bello Barmo; da kuma Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar, Sheikh Ahmad Kanoma.
“Sauran mambobin tawagar sun hada da Babangida Abubakar-Anka, Musa Ibrahim-Yau, da Hajiya Asiyatu Suleiman” in ji sanarwar.