• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hakkinmu Ne Mu Kawo Karshen Masu Kwacen Waya (I)

by Rabi'at Sidi Bala
2 years ago
in Rahotonni
0
Hakkinmu Ne Mu Kawo Karshen Masu Kwacen Waya (I)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Fili na musamman wanda ya ke bawa kowa damar tofa albarkacin bakinsa game da abin da ya ke ci masa tuwo a kwarya. Abba Abubakar Yakubu ya bayyana abin da ya ke damunsa cikin zuciya game da masu kwacen waya, inda ya fara da cewa:

Musa Sani Aliyu wanda aka fi sani da Musa Khan, ma’aikaci ne a gidan rediyon Jalla da ke birnin Kano. Watarana da daddare misalin karfe tara, a kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya tashi daga wajen aikinsa a daidai kan titin Club Road kusa da ofishin Kwastom, yayin da yake tafiya wasu batagari a kan babur suka sha gabansa yayin da suka nemi ya bada wayar da ke jikinsa, kafin ya sa hannu ya zaro wayar daga aljihunsa, sai daya daga cikin su ya fitar da wata wuka da ke jikinsada aka yi wa  kira ta musamman, ya sare shi a hannu. Zafin wannan saran ya sa Musa ya yi kuwwa domin neman taimako, ganin yadda jama’a suka fara nufowa wajen ya sa nan da nan barayin suka hau babur dinsu suka gudu. Ganin yadda jini ke zuba daga jikinsa inda suka sare shi sai aka garzaya da shi asibiti, domin ceto rayuwarsa. Musa Khan daya ne daga cikin daruruwan mutanen da suka tsallake rijiya da baya, yayin harin da ‘yan daba masu kwacen waya suka kai musu a lunguna da anguwanni daban daban na cikin birnin Kano, da sauran manyan biranen arewacin kasar nan.

Rahotannin da ke fitowa daga jihohi daban daban, irin su Kano, Kaduna, Katsina, Filato, Bauchi, Gombe, Adamawa da sauran birane da dama na bayyana cewa, ana samun munanan hare hare daga miyagun matasa wadanda shekarunsu ba su wuce 14 zuwa 25 ba, da ke dauke da muggan makamai kuma suke far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a kan tituna, da lunguna, har da cikin ababen hawa da gidaje, suna kwace musu wayoyinsu na hannu da wasu abubuwa da suka mallaka, wani lokaci ma an ce har ruwa mai guba na asid suke watsawa mutane, don jikkata su da yi musu lahani, har ma da kisan gilla.

A wasu lokutan wadannan matasa kan yi amfani da wuraren taruka kamar na siyasa, biki ko kuma idan an samu cinkoson ababen hawa a kan tituna sai su yi amfani da makami kamar wuka, adda, musilla, kaho, da wasu makamai masu ban tsoro, wajen yi wa mutane kwace. Yayin da suke wa mutane barazana a kan idan har basu bayar da abin da suke bukata ba sai sun yi musu rauni ko ma su hallaka su baki daya. Kuma abin takaici a yayin da suke wannan mummunar dabi’ar ba sa kyale yara, da mata, ballantana dattijai masu rauni.

Wasu daga cikin mazauna birnin Kano sun ce irin wannan kwace na waya ba wai na kan hanya kawai ake yi wa ba, a kan je har gida a yi sallama da mutum sannan a nemi ya bayar da wayarsa idan bai bayar ba sai a sa masa makami, a jikkata shi ko a kashe. Wasu rahotanni na bayyana cewa a kowacce rana a kalla mutane 15 ne suke gamuwa da ibtila’in sara da wuka ko wani makami ta dalilin kwacen waya a Jihar Kano. Yayin da a wata guda ake samun mutanen da tsautsayi ke fadawa kansu ta dalilin kwacen waya da yawan su ya kai 450. A daidai lokacin da nake wannan rubutu masu kwacen waya sun kashe mutane biyu cikin mako guda a Jos, ban da wadanda ake jikkatawa kusan a kowacce rana. Abin da yake kara daga hankalin masu fada a ji, da ke tattaunawa kan hanyoyin da za a bi a shawo kan wannan matsala da ke neman gagarar jami’an tsaro da ‘yan banga, duk kuwa da kokarin da suke yi ba dare ba rana, don kama masu aikata irin wannan danyen aikin da gurfanar da su gaban kuliya.

Labarai Masu Nasaba

Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi

Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro

Malam Nura Alhassan shi ne shugaban wata kungiyar matasa ta Jos Peace Banguard, wacce ke taimakawa wajen wayar da kan matasa masu harkar daba da shaye shaye, da canza musu tunanin su daga mummunar hanyar da suke kai, don su zama mutanen kirki kuma ‘yan kasa nagari. A wata ganawa da muka yi da shi ya bayyana min cewa, wannan matsala ta kwacen waya da ke dada ta’azzara na kara daga musu hankali sosai, musamman ganin a baya an samu saukin matsalar sakamakon kokarin da suka yi na hada kan kungiyoyin matasa ‘yan daba masu gaba da juna tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, inda aka sasanta su tare da kulla yarjejeniyar daina rikici a tsakaninsu, wanda sau da dama ke kaiwa ga kashe kashe da sare saren juna. Amma tun farkon wannan shekarar ta 2023, harkar fadan daba da kwacen waya ta sake kunno kai, musamman bayan dawowar harkokin siyasa.

Malam Nura ya ce, duk da yake jami’an tsaro na nasu kokarin amma ba za a nade hannu a sa musu ido ba, dole ne za su sake yunkurawa su ga sun gayyato tubabbun ‘yan daba da a baya suka yi ta fafutukar ceto su daga wannan mummunar hanya, domin amfani da su wajen zakulo kangararrun yaran da aka sani suna wannan abin da nufin zama da su don a dakile ci gaba da wannan mummunar halayya. Ya dora alhakin dawowar harkokin ‘yan daba da amfani da makamai da yara matasa ke yi kan wasu baragurbin ‘yan siyasa da ke sanya matasan cikin gurbatacciyar rayuwa ta shaye shaye da kai hari kan abokan adawa, a duk lokacin da kudaden da suka saba bai wa yaran ya kare ko suka dakatar da ba su, shi ne suke komawa fashi da makami, da kwacen wayoyi don su samu abin sayen kayan maye.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Kwacen Waya
ShareTweetSendShare
Previous Post

Tsokaci Kan Maza Masu Boye Bayanan Kansu Wurin Neman Aure

Next Post

Abin Haushi, Mata Sun Mayar Da Maza Tamkar Bola

Related

Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi
Rahotonni

Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi

4 weeks ago
Janar Tiani Ya Fara Sabon Mulkin Shekaru Biyar A Nijar
Rahotonni

Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro

1 month ago
An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya
Rahotonni

An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya

1 month ago
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa
Rahotonni

Amurka Ta Sayi Kayayyakin Nijeriya Na Dala Miliyan 643 A Wata 2 – Rahoto

1 month ago
Gwamnoni 20 Na Fuskantar Matsin Lambar NULGE Kan Rashin Aiwatar Da Mafi Karanci Albashi
Rahotonni

Gwamnoni 20 Na Fuskantar Matsin Lambar NULGE Kan Rashin Aiwatar Da Mafi Karanci Albashi

1 month ago
Tinubu
Manyan Labarai

Yadda Tinubu Ya Shirya Wa Kansa Mafitar Siyasa Kafin Zaben 2027

2 months ago
Next Post
Abin Haushi, Mata Sun Mayar Da Maza Tamkar Bola

Abin Haushi, Mata Sun Mayar Da Maza Tamkar Bola

LABARAI MASU NASABA

gaza

Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa

May 14, 2025
Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

May 14, 2025
Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

May 14, 2025
Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

May 14, 2025
Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

May 14, 2025
JAMB Ta Amince Da Maki 140 Da 100 Mafi Karancin Maki Na Shiga Manyan Makarantu

JAMB: TangarÉ—ar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025

May 14, 2025
A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka

A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka

May 14, 2025
ÆŠan Wasan Super Eagles Na Tsaka Mai Wuya Bayan An Yi Masa Tiyata

ÆŠan Wasan Super Eagles Na Tsaka Mai Wuya Bayan An Yi Masa Tiyata

May 14, 2025
Tattalin ArziÆ™in Nijeriya Ya BunÆ™asa, Amma Farashin Kayayyaki Na Ci Gaba Da Tashi – Bankin Duniya

Tattalin ArziÆ™in Nijeriya Ya BunÆ™asa, Amma Farashin Kayayyaki Na Ci Gaba Da Tashi – Bankin Duniya

May 14, 2025
Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar

Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.