Hadisai da suke magana kan hakuri da afuwar Annabi (SAW) lokacin da yake da cikakken iko kan komai wurin zartar da hukunci, ya fi karfin ace za a zo da su baki daya. Amma ya isa ma’auni a ce cikin Kabilar Kuraishawa ya taso kuma ya fara kira da a bi Ubangiji a cikinsu, wautar Jahiliyya a fili take a cikinsu har Allah ya taimake shi ya dora shi a kansu kuma ya hukunta shi a kansu.
Dukkan kabilar Kuraishawa sun yi tsammanin Annabi (SAW) zai karar da kabilarsu ne gaba daya a lokacin Fat’hu Makkah, sai ya ce musu “me kuke tsammani daga gare ni?”, sai suka ce masa “kai dan’uwa ne mai karamci kuma dan dan’uwa mai girma”, sai ya yafe musu ya yi musu irin ta Annabi Yusufa da ‘yan uwansa, “la tasriba alaikumul yauma…” an yafe muku, babu wani zargi a gare ku.
Sayyadin Anas, ya ce, yayin da Annabi (SAW) ya yi nufin zuwa Umra bayan yakin Badr, ya isa Hudaibiyya, sai samarin Makkah su 80 suka kawo masa hari cikin dare amma ba su yi nasara ba duk an cafke su, Annabi (SAW) ya ‘yantasu duka duk da cewa sun yi nufin kashe shi ne. Sabida haka, sai Allah ya saukar da aya yana cewa “wahuwallazi kaffa aidiyahum ankum wa aidiyakum anhum bi badni makkata min ba’adi an azfarakum alaihim,wa kanallahu bima ta’amaluna basira” Allah shi ne wanda ya rike hannayensu a gareku (ba za su iya cutar da ku ba) kuma ya rike hannunku a gare su (ba ku karkashe su ba) yayin da ya dora ku a kansu, Allah masani ne a kan duk abin da kuke shiryawa.
Manzon Allah ya fada wa Abu Sufyan (sirikinsa ne kuma kwamandan yaki da ya dinga shiryo wa Annabi (SAW) yaki kuma shugaban cutar da Annabi (SAW) lokacin ana zaman Makkah) yayin da aka kama shi a yakin Fat’hu Makkah, “kaiconka, kai har yanzun ba ka yarda Allah shi ne daya ba kuma ni Manzonsa ne?”, cikin taushin magana Annabi ya fada masa, sai Abi Sufyan ya ce “na ba da iyayena fansa a gareka, mamakin irin taushin zuciya da hakurinka da sada zumuncinka da karamcinka, yau ranar ramuwa ce amma duk ka nuna wadannan kyawawan halayen.”
Amma in mun sauya akalar karatunmu zuwa ‘Baiwar Annabi (SAW)’ za mu ga babu wani kamarsa.
Baiwa ana fassarta da ciyarwa ko kyauta da tsururi ko barin hanyar da a karshenta za a yi da-na-sani ko kuma za ta iya zubar da darajar Mutum. Ma’ana, baiwa ita ce kyauta.
Annabi (SAW) a cikin dukkan kyawawan halaye ba a kamanta shi da kowa.
Jabir dan Abdullahi (RA) yana cewa, ba a taba tambayar Annabi (SAW) da wani abu ba ya ce babu.
Abdullahi dan Abbas (RA) yana cewa “Annabi (SAW) ya kasance mafi baiwar Mutane da alkairi, lokacin da Annabi ya fi baiwa, shi ne lokacin watan Azumin Ramadana, ya kasance idan ya hadu da Mala’ika Jibrilu, Mala’ika Jibrilu yana zuwa suna Musaffan Karatun Alkur’ani da Annabi (SAW) duk watan Ramadana sau daya, sai shekarar wafati ce suka yi sau biyu.
Shi ya sa, duk musulmai suna da baiwa da kyauta amma in watan Ramadana ya zo sai ka ga sun kara ninkawa.
An karbo hadisi daga Anas khadimin Manzon Allah (SAW) ya ce, wani Mutum ya nemi kyauta daga Manzon Alla (SAW), sai ya ba shi Tumaki tsakanin duwatsu biyu cike da dabbobi amma Annabi sai da ya ba shi dukkansu (SAW). Wanann ya faru ne a lokacin yakin Hunaini, Sahabin shi ne Safwan bin Umayya. Annabi ya gan shi yana ta kallon tumakin, sai ya tambaye shi, sun burge ka ne? sai ya ce Ya Rasulallahi wane Balarabe ne zai ce bai son wannan, take Annabi ya ce masa ya dau sanda ya kora su ya bar masa. Sai Safwan ya koma wurin mutanensa ya ce musu ku Musulunta sabida ‘Muhammad’ (SAW) yana bayar da kyauta irin wacce ba ya tsoron talauci.
Wata rana Manzon Allah (SAW) ya bai wa Abu Sufyan Rakumi 100 a lokaci daya, ya bayar da dukiya mai yawa da ba a san adadinta ba da aka samo ganima a yakin Hunaini.
Yakin Hunaini, yaki ne da ya kasance bayan fitowar Annabi (SAW) da rundunar yaki sama da 10,000 don bude Makkah, amma kuma sarkin Hunain ya karya alkawari da Annabi (SAW), ya ji labarin rundunar da Annabi (SAW) ya fito da ita, sai ya tara ninkin ta Annabi Uku (30,000) kuma ya ce kowannensu ya fito da duk dukiyar da ya mallaka da kuma iyalansa (Mata da Yara), rundunar Hunaini dukkansu maharba ne.
Bayan Annabi (SAW) ya bude Makkah, ya samu karin mayaka, sai ya nufi Hunaini, wasu daga cikin Sahabbai suka fara alfahari cewa “Yau babu wata runduna da za ta iya kayar da mu”, bayan Annabi ya fada wani kwari a hanyar zuwa Hunaini, ashe duk rundunar maharba su 30,000 suna sama kowanne da kibiya a hannu, kawai sai suka yo ruwan kibiyoyi ga sahabbai, nan fa kowa ya arta a guje sai Mutum 100 kacal, Annabi (SAW) ya watsa musu kasa duk ta cike idanuwan maharban sannan ya sa Baffansa Abbas ya kira Mutanen Madina. Allah ya ba wa Annabi (SAW) da rundunarsa Nasara, Kafirai sun bar dukiyoyinsu da Iyalansu.
Wannan dukiya da suka bari mai yawa, Annabi (SAW) ya jira ko za su dawo su Musulunta ya mayar musu da dukiyarsu amma ba su dawo a lokaci ba har sai da Annabi (SAW) ya rabar da dukiyar baki daya sannan suka dawo.
Annabi (SAW) ya nemi zabinsu a kan wanda ya fi ,muhimmanci a wurinsu, Dukiyarsu ko Iyalansu, sai suka zabi Iyalansu, an ce Annabi ya maida musu da ‘yan mata sama da 6,000.
Annabi (SAW) ya ba wa baffansa Abbas dukiya (zinare) ya dauka iya karfinshi, an kawo wa Annabi (SAW) daga ganimar yakin kudi Dirhami 90,000, Annabi (SAW) ya sa aka shimfida tabarma a Masallaci, har sai da ya rabar da kudin gaba daya, Abbas ya ce ya Dana a yakin Badr sai da kasa na biya fansar Mutum Uku, kai ka maida ni Talaka don haka yanzu ga kudi a maida min da kudina, shi ne Annabi (SAW) ya hore shi da ya diba zinare iya karfinshi. Bayan an gama rabo sai wani ya zo ya ce Ya Rasulallahi ina nawa? Annabi ya ce masa komai ya kare amma ya je ya ci bashi zai biya masa in an samu kudi.
Sai Sayyadina Umar ya ce Ya Rasulallahi Allah bai dora maka abin da ba zaka iya ba, Annabi (SAW) ya ki wannan maganar, sai wani daga cikin Sahabbai ya ce Ya Rasulallahi ka ciyar, kar ka ji tsoron wani talauci daga Ubangjin Al’arshi, sai Annabi (SAW) ya yi farin ciki kuma aka ga bishara a fuskarsa.
An karbo daga Mu’awwizu bin Afra’a (Sadaukin Badr) yana cewa, wata rana na zo wurin Annabi (SAW) ina dauke da faifai da Dabino a kai, hakikanin Hadisin ‘yarshi ce ya aiko ba shi ne ya zo da kanshi ba, ta ce na zo wurin Annabi (SAW) da faifai akwai Dabino danye da Bulubutu danye wanda bai girma sosai ba a kanshi, sai Annabi (SAW) ya ciko hannunsa da kayan kwalliya na Mata (Awarwaro) na zinari ya ba ni.
Khadiminsa Anas, ya kasance yana cewa, Annabi (SAW) ba ya ajiye komai sabida gobe a kan-kansa amma yana ajiye wa Matansa abincin Shekara, don haka in sun ba shi ya gode, in ba su bashi ba, daman nasu ne.
Yana daga cikin kyautar Annabi (SAW), wata rana wani ya taba zuwa wurinsa yana neman taimako Annabi kuma (SAW) lokacin babu, sai ya nemo rancen rabin masaki na Dabino ya bashi. Wanda kuma ya bai wa Annabi (SAW) wannan rancen, da ya zo amsar bashinsa sai (SAW) ya ba shi Masaki cikakke. Annabi ya ce masa, rabin biyan bashi ne, dayan rabin kuma kyauta ce.