Ba dole bane a matsayinka na Malamai sai kana wani kaiyadadden hali bane za ka iya zama Malami mai halin kirki ba, sai dai kuma duk da hakan da akwai wasu abubuwan da za ka yi amfani dasu domin kai ma ka kasance Malamin da ake son koyi da kai saboda kai ma wanda ake ji da kai ne a bangaren ilimi.
1.Tafiya Da Duk Yadda Lamari yake
- Nijeriya Ta Yi Asarar Tiriliyoyin Naira Kan Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba – Gwamnati
- Matakin Amurka Na Kakaba Haraji Kan Kayayyakin Sin Ta Fakewa Da Batun Sinadarin Fentanyl Bai Dace Ba
Tafiya da duk yadda lamari yake shi ne abinda ake fi so daga wurin Malaman makaranta wadanda ake fatan za su ci gaba da bincike kan abubuwan da suka dacewa da dalibansu,bugu da kari kuma har ma gano ko sanin wadanda ba zasu amfanar da su ba.Idan Malaman makaranta suka kasance haka wato suna iya yin amfani da kowane irin salo na koyarwa wanda kuma zai taimakawa dalibai,ba tare da wata damuwa ba ko rasa sanin yadda za a dauki mataki.
2.Gane irin abinda ke damun wani
Iya gane irin halin da mutum yake ciki abin yin anan bai shi ne wuce kai ma/ ku ma ku nuna kuna cikin irin halin.A matsayinku na Malamai muhimmin abu ne ku zaman to kuna nuna cikin irin halin kuke maimakon ku nuna hakan ne bayan kuwa abin ba haka yake ba, alal misali,yin kokari na gano micece matsalar da kuma yadda za ayi maganinta wato dalilin da yasa dalibai suke kasancewa basu ganewa kamar yadda ‘yan’uwansu suke,ko ta zama kokarinsu ya ja baya sosai ba kamar yadda suka saba yi ba a baya,ko sune na baya a ajin.
3.Mai dauriya / hakuri
Hakuri yana da matukar kyau ace kana da shi a matsayinka na Malami ka kuma nunawa dalibai domin su ta shi da shi, wadanda kamar yadda aka yi bayani cikin maganar dabarun koyarwa,suna iya daukarka, a matsayin wanda za su rika yin koyi da kai saboda su koyi halinka na hakuri.Matukar akwai hakuri za a samu saukin yin aiki tare da kowadanne matsaloli ko fadi tashin da dalibi yake yi,wanda hakan na iya zama masa babban wani tarnaki wanda zai wuyar gano bakin zaren,ko kuma abin ya zama tamkar tafiyar Kura.
4. A rika yin abubuwan jawo ankali
Dalibai suna fara koyo ne tun lokacin da suke ‘yan yara hakan kuma ne ya basu damar fadawa Malamai cewar su gaji da yadda kai Malami/ko Malamai suke koya ma su.Matukar kana son ka yi dalilin yadda ajin na ka zai zama abin burgewa,don haka idan ka gano yadda lamarin yake,sai ka yi amfani da damar wajen kawo masu misalan ra’ayoyin da za su jawo hankalinsu,har abin ya shiga zuciyarsu da kuma maida hankalinsu kan abinda ake koya masu!
5.Rika saurare sosai
Yin saurare hakan na da amfani saboda gane matsalar da bada taimakon yadda za ayi maganin abin wato su matsaolin.Ka nemi a baka irin halin da ake ciki,bada kwarin gwiwa bil hakki da gaskiya, samar da hanyoyin da dalibai za su rika tuntubar ka a saukake,ka kuma tsaida hankalinka duk lokacin da kake saurare,ko wane lokaci ka yi kokarin gane manufa lokacin da ake yin magana,ka kuma lura dakyau yadda labarin zuciya yake lokacin d a kake magana ko ake yi maka.Yi kokarin sanin me yasa d a kuma dalilin da yasa za kayi hakan
6.Mai/ Masu son abinda suke koyawa
Masana ilimi ba wai kawai suna sha’awar aikin koyarwar bane bugu da kari ma suna da sha’awa ta daukar lokaci mai tsawo suna kasancewar su ta masu koyo,wanda irin haka yana nunawa a gwagwarmayar su ta masu koyarwa. Ci gaba da koyo da bunkasar kwarewar kwararru irin hakan yana matukar taimakawa ta yadda kwararru za su kasance koda yaushe suna cikin “shirin kota kwana”da kuma tunatar da Malamai da irin matsalolin duniya mai nuna cewa dalibansu na iya fuskanta,sai kuma samar da wata dama ta nuna damuwa da abubuwan da suke damun wasu.Kara gano lamurran dangane da muhimmancin daukar lokaci mai tsawo ana koyo,da kuma yadda dabarun hanyoyin koyo za su taimaka maku ku koyar ko kuma gane/gano sababbin abubuwan da suka shafi ilimi.
7.Su zama basu da nuna bambanci
Matsayinka na mai ilimi zaka kasance da alhakin koyarda dalibai masu bambancin fahimtar ita koyarwar.Idan za ka yi maganin nuna bambanci,da kuma yin adalci,akwai bukatar ka rika gwada bukatar dalibanka,ta hanyar da babu nuna wani fifiko,abinda yake bukatar kai ka ci gaba da yin bincike da kuma bada bayani kan yadda ka fahimci ko nazarci wasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp