Kamar yadda aka sani cewa kowace mace da irin kirar halittar da Ubangiji ya yi mata, amma tambayar a nan ita ce me ya sa mata ke murjewa su yi kiba bayan sun yi aure.
Wannan lamari ba bako ba ne ga dukkan al’ummar kasar Hausa. In muka duba za mu ga cewa da yawa daga cikin matan Nijeriya musammam yankin Arewa da zarar mace ta yi aure ba jimawa sai ka ga halittar jikinta ya fara sauyawa ta yi kiba ta murmure duk taya ni muni sun bace. A al’adance al’ummar kasar Hausa suna kallon wannan lamari a matsayin ci gaba ga mace saboda ana ganin cewar tana samun matukar kulawa a wurin mijinta.
- Za Mu Tabbatar An Hukunta Masu Zaluntar Kananan Yara Da Mata – Kwamishina Rabi Salisu
- Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Wa Matar Da ‘Yan Bindiga Suka Raba Da Muhallinta Shatara Ta Arziki
Amma sai dai abin tambaya a nan shi ne kulawar miji ita ce babbar magana da ke sa jikin mace ya canza ko kuwa akwai wasu abubuwa?
Tabbas kulawar miji na janyo sauyi ga halittar mace amma hakan bai isa dalili daya da za a ce shi ne ke janyo wannan sauyi ba.
Ga kadan daga cikin dalilan da ke sa mace samun sauyin halitta a gidan miji;
Samin kwanciyar hankali
A lokacin da mace ta yi aure za a ga cewa akwai wata kwanciyar hankali na musamman da za ta fuskanta wanda duk inda ta je ba za ta same ta ba sai a gidan miji ire-iren wannan sauyi sun hada da amarci, soyayya, sannan kuma cima mai kyau, wadannan abubuwa suna da matukar tasiri a canjin halittar mace, cikin kankanin lokaci za a ga mace ta murmure ta murje.
Sabuwar Rayuwa da kuma samun ‘yancin kai
Bayan soyayya a aure akwai kuma wasu tarin nauyi da zai hau kan mace wanda hakan kansa ta fahimci cewar girma da kulawar wasu mutane ya hau kanta kamar su rainon ciki, haihuwa da kuma renon yaron da za ta haifa. Wannan sauyin da kwanciyar hankali suma suna kara taimaka wa mace wajen zama babbar mata. Sai a ga cikin kankanin lokaci mace ta murje ta yi jiki duk wasu jijiyoyi, kasusuwa, da kuma kwayar halittunta sun sami sauyi sun bude wanda hakan zai sa alamar kiba ta bayyana.
Rainon Ciki
Bayan hidimar aure akwai babbar hidima a gaban ma’aurata, wannan hidima ita ce daukar ciki. Haihuwa da aba ce mai matukar dadi da sa farin ciki kuma tana daga cikin abubuwa mafi sauki da ke kara wa mata budewar jiki ka ga sun yi kiba.
Daga lokacin da mace ta sami ciki to tabbas cin abincinta zai karu fiye da na da, za a ga idan a da tana cin karamin kwano to daga ta sami ciki sai ka ga abin ya canza, dole a nemo babban mazubi.
Mata yayin da suke da ciki suna matukar yin ciye-ciye sosai musamman abubuwa masu maiko wanda hakan ke sa jikin mace ya bude har ta yi jiki ta murmure.